Tinubu Ya Yi Magana bayan Amurka Ta Yi Ikirarin Kashe Kasurgumin Dan Ta'adda a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kashe babban kwamanda a kungiyar ISIS, Abu-Bilal Al-Manuki a yankin Tafkin Chadi
- Tinubu ya ce sojojin Najeriya da taimakon dakarun Amurka ne suka kai samame maboyar yan ta'addan kuma suka samu nasara
- Shugaban kasar ya gode wa Shugaba Donald Trump na kasar Amurka bisa goyon bayan da yake ba Najeriya a yaki da ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ta'addanci (ISIS) mai suna Abu-Bilal Al-Manuki, wanda aka fi sani da Abu-Mainok a Najeriya.
An kashe kasurgumin dan ta'addan ne a wani samame na haɗin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na Amurka a yankin Tafkin Chadi.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya tabbatar da kashe Abu Mainok
Tinubu ya tabbatar da halaka Abu Mainok ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.
Shugaba Tinubu ya bayyana aikin a matsayin babbar nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci tare da misali mai ƙarfi na haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
A cewar shugaban ƙasar, rundunar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka sun kai samamen cikin dare, inda suka kashe Al-Manuki tare da wasu manyan kwamandojinsa a yankin Tafkin Chadi.
Sojojin Najeriya da Amurka sun illata ISIS
Tinubu ya ce samamen ya yi wa ƙungiyar ISIS mummunar illa tare da sake tabbatar da aniyar Najeriya na ci gaba da matsa lamba kan ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a ciki da wajen ƙasar.
“Jajirtattun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka sun gudanar da wani gagarumin samame wanda ya yi wa ƙungiyar ISIS mummunar illa."
“Rahotannin farko sun tabbatar da kashe babban jagoran ISIS da ake nema ruwa a jallo, Abu-Bilal Al-Manuki wanda aka fi sani da Abu-Mainok, tare da wasu daga cikin manyan kwamandojinsa.”
- In ji Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu ya gode wa Amurka da Trump
Shugaban ya gode wa Amurka saboda haɗin gwiwar da take bayarwa wajen cimma manufofin tsaro na bai ɗaya, tare da nuna godiyarsa ga Shugaban Amurka Donald Trump bisa jagoranci da goyon bayan da yake bayarwa.
“Najeriya na matuƙar yaba wa da wannan haɗin gwiwa da Amurka wajen bunƙasa manufofin tsaro na bai ɗaya.
"Ina miƙa godiyata ga Shugaba Trump saboda jagoranci da goyon bayan da yake bayarwa a wannan yunƙuri,” in ji Tinubu.

Source: Getty Images
Ya kuma yabawa jami’an sojin ƙasashen biyu bisa ƙwarewa da jarumtakar da suka nuna yayin gudanar da samamen, yana mai bayyana fatan cewa za a ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare masu ƙarfi kan sansanonin ‘yan ta’adda.
Sojoji sun musanta kashe fararen hula
Kun ji cewa, hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahoton da ake yadawa cewa jirgin yakin sojoji ya yi kuskuren yin luguden wuta kan jama'a a kasuwar Tumfa, jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027
Ta bayyana cewa babu tabbatacciyar shaida cewa fararen hula sun mutu a harin sama da jirgin sojoji ya kai kasuwar, inda ta ce an kashe yan ta'adda da dama.
Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Amnesty International ta ce adadin wadanda suka mutu ya haura 100, zargin da rundunar sojin ta ce ba gaskiya ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

