Duk da Ƙaryata Amurka, An Tabbatar da Hannun Trump a Hallaka Jagoran ISIS a Najeriya
- 'Dan majalisar Amurka ya ce shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ne ya ba da umarnin kai farmakin haɗin gwiwa a Najeriya
- A baya-bayan nan ne Najeriya da Amurka da ya kashe wani babban jagoran ISIS mai Abu-Bilal al-Minuki a yankin Tafkin Chadi bayan harin
- Hukumomin tsaro sun danganta al-Minuki da ayyukan Boko Haram daga ciki har da satar ‘yan matan makarantar Dapchi a 2018
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. United States – 'Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya bayyana cewa shugaban ƙasar Amurka da amincewa da wani samame na haɗin gwiwar Najeriya da Amurka.
Najeriya ta bayyana cewa an kai harin da ya yi sanadin kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda ake bayyana a matsayin mataimaki na biyu mafi girma a ƙungiyar ISIS ta duniya.

Source: Twitter
A hirarsa da News Nation, Moore, wanda ke aiki a kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilan Amurka, ya bayyana cewa farmakin na daga cikin ƙarin haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci tsakanin Najeriya da Amurka.
Moore ya yabi Trump
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Moore ya ce gwamnatin Trump ta mayar da hankali sosai kan yaƙi da ta’addanci da kuma kare al’ummomin da hare-haren masu tsattsauran ra’ayi suka shafa a Najeriya.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Amurka ta ƙarfafa hulɗa da Najeriya bayan da aka ayyana ƙasar a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta dangane da zarge-zargen take haƙƙin addini.
Moore ya ce Trump ya umarce shi da ya binciki halin da ake ciki a Najeriya, lamarin da ya kai shi ziyarar tattara bayanai kafin ya miƙa rahoto ga fadar White House kan matsalolin tsaro da kare fararen hula.
A cewarsa, shawarwarin da aka bayar sun fi karkata ne wajen ƙarfafa kariya ga al’ummomin da rikicin masu tsattsauran ra’ayi ya shafa tare da inganta haɗin kai a ayyukan yaƙi da ta’addanci.
Amurka na aiki da Najeriya
Riley Moore ya bayyana cewa Amurka na aiki da Najeriya tun gabanin bullar kungiyar Boko Haram kuma ana ci gaba da aikin hada kai game da rashin tsaro a kasar.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa an kashe Abu-Bilal al-Minuki a wani farmaki da ta bayyana a matsayin wanda aka tsara cikin tsanaki a yankin Tafkin Chadi.
Daraktan yaɗa bayanan tsaro, Samaila Uba, ya ce mamacin na ɗaya daga cikin ƙwararrun jagororin mayaƙan masu tsattsauran ra’ayi, inda ya taka rawa a harkokin ƙera makamai, bunƙasa jiragen marasa matuƙi da kuma yaɗa farfaganda.
Sai dai ta tabbatar da cewa sojojin kasar nan ne suka kai wannan hari wanda ya yi sanadin kawar da kasurgurmun dan ta'addan.
Amurka ta kawo hari Najeriya
A wani labarin, mun wallafa cewa dakarun sojin Amurka da na Najeriya sun sake kai farmaki kan mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya inda ake fama da matsalar tsaro.
Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afirka (AFRICOM) da hedkwatar tsaron Najeriya sun tabbatar da kai hare-haren yau Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 yayin da ake ci gabba da hadin gwiwa a tsakanin kasashen.
Hedkwatar tsaro ta kuma sake jaddada kudurinta na kare ikon Najeriya da tsaron kasar, tana mai cewa za ta ci gaba da daukar matakin murkushe ta'addancin da ke ci gaba da hana jama'a zaman lafiya
Asali: Legit.ng


