"Babu Hujja," Sojojin Najeriya Sun Yi Magana kan Zargin Kashe Fiye da Mutane 100 a Zamfara
- Babbar hedkwatar tsraon Najeriya ta ce babu tabbatacciyar shaida cewa fararen hula sun mutu a harin sama da jirgin sojoji ya kai Tumfa, jihar Zamfara
- AFP da Amnesty International sun ce mutane da dama sun mutu a harin, wanda ake zargin jirgin sojoji ya yi kuskuren jema bam a kasuwa
- Hedikwatar tsaro ta ce labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne domin babu wata hujja, tana mai cewa an kai harin ne kan taron jagororin ‘yan ta’adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahoton da ake yadawa cewa jirgin yakin sojoji ya yi kuskuren yin luguden wuta kan jama'a a kasuwar Tumfa, jihar Zamfara.
Babbar hedkwatar sojojin ta ce babu wata “tabbatacciyar” ko “ingantacciyar” hujja da ke nuna cewa fararen hula sun mutu sakamakon harin da aka kai kasuwar Tumfa da ke karamar hukumar Zurmi.

Source: Twitter
Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Michael Onoja ne ya musanta labarin a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 13 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda The Cable ta kawo.
Abin da ake zargin sojoji sun yi a Zamfara
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa akalla mutum 72 zuwa 1000 ne suka mutu bayan harin bama-bamanda sojoji suka kai kan yan kasuwa ranar Lahadi.
Rahoton ya ambato wani jagoran al’umma mai suna Garba Ibrahim Mashema yana cewa gawarwakin wasu daga cikin wadanda suka mutu sun “tarwatse ta yadda ba za a gane su ba.”
“Yana da wahala a tantance adadin wadanda suka mutu yanzu. Kowa na zuwa kasuwar, mazauna gari da ‘yan bindiga. Mutane suna cikin mawuyacin hali a hannun ‘yan bindigar,” in ji shi.
Amnesty ta ce an kashe mutum 100
Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Amnesty International ta ce adadin wadanda suka mutu ya haura 100, yayin da mutane da dama da suka jikkata ke samun kulawa a asibiti.
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa s daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa, an yi jana’izar mutum 80 a lokaci guda.
DHQ ta musanta kashe fararen hula
Sai dai kakakin Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ), Manjo Janar Michael Onoja, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa fararen hula sun mutu a harin.
Ya ce an kai harin ne bisa dokokin kasa da kasa, kuma an kai shi ne kan “wani babban taron jagororin ‘yan ta’adda” a kauyen bayan samun bayanan sirri daga wurare daban-daban.
“Babu wata tabbatacciyar hujja ko bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da mutuwar fararen hula,” in ji Onoja.

Source: Original
Ya kara da cewa yanayin aikin ya sanya tantance adadin wadanda suka mutu cikin gaggawa ya zama da wahala, amma bincike ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama.
Gwamnatin Zamfara ta yi martani
A baya, kun ji cewa gwamnatin Zamfara ta yi karin haske kan harin da sojoji suka kai wata kasuwa, wanda ake zargin ya yi ajalin fararen hula sama da 100.

Kara karanta wannan
"Yara na 3 sun mutu," Magidanci ya sabawa bayanin sojoji kan kuskuren jefa bam a Neja
Gwamnatin Zamfara ta ce yankin da aka kai harin sanannen maboyar ‘yan bindiga ne da jami’an tsaro ke bibiyarsu.
Mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Danmanga, ya ce gwamnatin jihar ba ta san akwai kasuwa a yankin ba.
Asali: Legit.ng

