Babban Kwamanda da Daruruwan Yan Ta’adda da Harin Amurka, Najeriya Ya Yi Ajali
- Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske kan harin Amurka da hadin guiwar Najeriya wanda ya yi ajalin yan ta'adda
- Rundunar sojoji ta bayyana cewa hare-haren haɗin guiwa da Amurka suka kai sun kashe mayaƙan ISIS 175 a Arewa maso Gabas
- Hukumar tsaron ta tabbatar da cewa hare-haren sun lalata sansanonin ’yan ta’adda tare da karya hanyoyin kuɗi da kayan aikinsu a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana yadda harin Amurka da hadin guiwar Najeriya ya yi ajalin babban kwamanda a Arewa maso Gabas.
Rundunar tsaro ta ce hare-haren haɗin guiwa da rundunar AFRICOM ta Amurka suka kai sun kashe mayaƙan ISIS 175.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata sanarwa ta rundunar ta wallafa a shafinta na X a yau Talata 19 ga watan Mayun shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya
A cikin sanarwar da Daraktan yaɗa bayanan tsaro, Birgediya Janar Samaila Uba ya fitar, an bayyana harin a matsayin babban nasara.
Harin Amurka, Najeriya ya hallaka yan ta'adda
Sanarwar ta ce hare-haren da aka fara kwanaki kaɗan da suka gabata sun lalata shingayen ’yan ta’adda da ma’ajiyar makamai da kayayyakin yaƙi.
Sojojin sun kuma ce hare-haren sun lalata cibiyoyin sufuri, kayan aikin soja da hanyoyin kuɗaɗen da ke tallafa ayyukan ISIS a yankin.
Hedikwatar tsaron ta ce ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe shi ne Abu-Bilal al-Minuki, wanda aka bayyana a matsayin babban ɗan ISIS a duniya.
Sojoji sun ce al-Minuki yana taka muhimmiyar rawa wajen shirya hare-hare, samar da kuɗi, ɗaukar mayaƙa da tsara ayyukan ta’addanci a duniya.

Source: Facebook
Yadda harin ya raunana ayyukan kungiyar ISIS
Sanarwar ta ƙara da cewa mutuwarsa ta girgiza tsarin jagoranci da ayyukan ISIS tare da raunana shirye-shiryen hare-haren ƙungiyar.
Hedikwatar ta kuma bayyana wasu jagororin ta’addanci da aka kashe da suka haɗa da Abd-al Wahhab da Abu Musa al-Mangawi da sauransu.
An kuma kashe Abu al-Muthanna al-Muhajir, wanda ake zargi da kula da yaɗa bidiyoyi da harkokin yaɗa labaran ISIS a yankin.
Sojoji sun ce zuwa ranar 19 ga Mayun 2026, bayanai sun nuna cewa mayaƙan ISIS 175 ne aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar.
Hedikwatar tsaron ta bayyana cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ta’addanci lamba a sassan ƙasar nan.
Ta kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa haɗin gwiwa da rundunar AFRICOM zai ci gaba domin kare tsaron ƙasa da zaman lafiyar yanki.
Al-Minuki: Rundunar ta saba da bayanan Amurka
An ji cewa hedikwatar tsaro ta yi karin haske game da rahotanni kan kisan hatsabibin dan ta'adda, Abu Bilal Al-Minuki da aka yi.
Rundunar ta bayyana gaskiya kan rawar kasar Amurka da ta ke ikirarin ta hannunta aka kashe kashe shugaban ISIS Abu Bilal Al-Minuki.
Janar Michael Onoja ya ce Amurka ta bayar da tallafin bayanan sirri, sa ido da bincike kawai, ba tare da tura sojojinta ba.
Asali: Legit.ng
