Alkawarin Gwamnan Kebbi ga Iyalan Jami'an Yan Sanda da Yan Bindiga Suka Kashe
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya yi alkawarin tallafa wa iyalan ’yan sanda 10 da ’yan ta’adda suka kashe yayin gudanar da ayyukan tsaro
- Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da tawagar babban sufeton ’yan sanda, Olatunji Disu, ta kai masa ziyarar ta’aziyya a Birnin Kebbi
- Mataimakin babban sufeton ’yan sanda, Umar Dada, ya ce rundunar za ta ƙara ƙoƙari wajen kama waɗanda suka kai harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi nuna damuwa game da harin yan bindiga da suka yi ajalin jami'an yan sanda har guda 10.
Gwamnatin ta yi alkawarin tallafa wa iyalan ’yan sanda 10 da wasu mutanen da ’yan ta’adda suka kashe a yankin Rafin Makuku, ƙaramar hukumar Sakaba.

Source: Facebook
Gwamna Nasir Idris ya yi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar Babban Sufeton ’Yan Sanda, Olatunji Disu, ta kai masa ziyarar ta’aziyya, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Gwamnan APC ya ƙaƙaba harajin N150m kan Bola Tinubu da wasu yan takara a zaben 2027
Gwamna ya jajantawa iyalan yan sanda
Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda, Umar Dada, ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan gwamnatin Kebbi da ke Birnin Kebbi domin jajantawa gwamnan da jama’ar jihar.
Gwamna Idris ya jajanta wa rundunar ’yan sandan Nijeriya kan rasuwar jami’an, yana mai cewa sun rasa rayukansu ne yayin gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ba su.
Ya ce an tura jami’an yankin ne domin su taimaka wa sauran hukumomin tsaro wajen yaki da ta’addanci da sauran nau’o’in aikata laifuka.
Gwamnan ya ce:
“Ina mika ta’aziyyata ga Babban Sufeton ’Yan Sanda da daukacin rundunar kan wannan mummunan rasuwar jami’an.“
Al’ada ce a Kebbi mu tallafa wa iyalan jami’an tsaro da suka rasa rayukansu yayin gudanar da ayyukan kasa, Gwamnatin Kebbi za ta taimaka wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu.”

Source: Original
An yi ta'aziyya ga shugaban yan sanda
Tun da farko, DIG Dada ya isar da sakon ta’aziyyar Babban Sufeton ’Yan Sanda ga gwamnan, al’ummar Kebbi da kuma iyalan jami’an da suka mutu.

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya jawo wa kansa, kalamansa kan zaben Osun sun jefa shi cikin matsala
Ya tabbatar wa gwamnan cewa rundunar ’yan sanda za ta kara kaimi wajen kamo wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya ce:
“Ku kasance da tabbacin cewa ba za mu sassauta kokarinmu ba. Za mu kama duk wadanda ke da hannu wajen kai harin tare da gurfanar da su."
Mataimakin babban sufeton ya yaba wa gwamnatin Kebbi kan ci gaba da tallafa wa rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar, cewar Tribune.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a kafa wata rundunar ’yan sanda ta musamman a Kebbi domin karfafa ayyukan tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Tawagar ’yan sandan ta ziyarci Kebbi ne bayan kashe jami’an ’yan sanda 10 da wasu mutane yayin wata arangama da ’yan ta’adda a yankin Rafin Makuku.
Alkawarin gwamnan na tallafa wa iyalan jami’an da suka mutu ana sa ran zai taimaka musu wajen fuskantar mawuyacin hali bayan rasa ’yan uwansu.
Yan bindiga: Gwamna ya roki rundunar sojoji
A wani labarin, an ji cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta kawar da ’yan bindiga da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin ziyarar ba-zata da ya kai sansanin sojoji da ke Yauri, inda ya yaba da jajircewarsu wajen kare al’umma.
Ya ce karin sojojin da aka tura Kebbi zai karfafa yaki da ’yan bindiga, musamman a yankin Yauri, Shanga da Ngaski.
Asali: Legit.ng
