Sojojin Amurka Sun kai Hari Najeriya, Trump Ya Ce An Kashe Abu Bilal al Minuki

Sojojin Amurka Sun kai Hari Najeriya, Trump Ya Ce An Kashe Abu Bilal al Minuki

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce an kashe wani babban jigo a kungiyar IS, Abu-Bilal al-Minuki da aka sa masa takunkumi a shekarun baya
  • Donald Trump ya rubuta cewa an kashe Abu-Bilal al-Minuki a Najeriya yayin wani samame na hadin gwiwa da ya hada dakarun Amurka da na Najeriya
  • Trump ya ce al-Minuki ne mataimakin shugaban kungiyar IS na biyu a duniya baki daya kuma kashe shi zai kawo karshen hare-harensa a yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa sojojin kasar shi da na Najeriya sun kashe wani babban dan kungiyar IS.

Hakan na zuwa ne bayan shafe watanni da sojojin Amurka suka yi a Najeriya da sunan za su taimaki kasar da yaki da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana bayan Amurka ta yi ikirarin kashe kasurgumin dan ta'adda a Najeriya

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump na bayani. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Donald Trump ya kashe dan ta'adda a Najeriya

A sakon da White House ta wallafa a X, ta ce Abu Bilal yana cikin manyan 'yan kungiyar IS na duniya.

“Ba zai sake addabar mutanen Afirka ko taimakawa wajen shirya hare-haren da za su kai hari kan Amurkawa ba,”

In ji Trump.

Shugaban Amurkan ya ce kawar da al-Minuki ya sa ayyukan kungiyar IS na duniya “sun ragu matuka.”

Trump ya nuna godiya ga gwamnatin Najeriya saboda hadin gwiwar da ta bayar a samamen da aka kashe al-Minuki.

Wane ne Abu Bilal al-Minuki?

Bayan Trump ya yi ikirarin kashe Abu Bilal, NDTV ta fitar da wasu muhimman abubauwa game da shi, musamman kan yake-yake.

Takunkumin Amurka a 2023

A cewar ofishin kula da kadarorin wajen Amurka da ke aiwatar da takunkumin tattalin arziki kan mutane da kungiyoyi kamar ‘yan ta’adda da masu safarar miyagun kwayoyi, an haifi al-Minuki a shekarar 1982 a jihar Borno da ke Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba tare da kashe kowa ba"; Obama ya fadi yadda ya kulla yarjejeniya da Iran

An sanya Abu-Bilal al-Minuki cikin takunkumin Amurka a shekarar 2023 saboda alakarsa da kungiyar IS, wadda ke da babban tasiri a wasu sassan Yammacin Afirka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, yayin da ta sanya shi cikin jerin “’yan ta’addan duniya” a shekarar 2023, ta bayyana shi a matsayin wani babban jagoran ISIS da ke yankin Sahel.

An sanya al-Minuki, dan Najeriya, cikin jerin “manyan ‘yan ta’addan duniya na musamman” karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Amurka, Joe Biden a shekarar 2023.

Matsayinsa a cikin ISIS

A cewar wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta, al-Minuki yana zaune ne a yankin Sahel kuma yana jagorantar jami’ai a bangaren Tafkin Chadi na ofisoshin ISIS.

Rahotanni sun ce Al-Minuki ya rike matsayin kwamandan yanki a ISIS tun bayan kashe shugaban ISWAP, Mamman Nur, a shekarar 2018.

Bola Tinubu da sojojin Amurka
Wasu sojojin Amurka da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Alakar Al-Minuki da Abubakar Shekau

A cewar masana tsaro, Al-Minuki yana da matsala a alakarsa da shugaban Boko Haram da ya mutu a baya, Abubakar Shekau.

A wani lokaci tsakanin Maris din 2015 da farkon shekarar 2016, Shekau ya ki amincewa da bukatar ISIS ta aika mayaƙa zuwa Libya.

Kara karanta wannan

Yahudawa sun bankawa masallaci, motoci wuta yayin ibada a Isra'ila

Sai dai an ce, maimakon haka, Al-Minuki, wanda ke matsayin kwamandan yankin Tafkin Chadi na ISWAP, ya aika mayaƙan.

An cafke dan ta'adda a Oyo

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sanda ta kama wani dan bindiga da ake zargi yana garkuwa da mutane a Oyo.

Kakakin 'yan sandan jihar ya bayyana cewa sun kai farmaki maboyar 'yan ta'addan ne bayan sun kai hari gidan wani mutum sun sace shi.

Rahoton 'yan sanda ya nuna cewa an dabarar kama dan bindigar ne bayan sun bukaci a ba su kudin fansa har Naira miliyan 10 kafin su saki mutumin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng