An Soki Ganduje kan Kalamai Mabambanta game da Sahihancin Sarautar Sanusi II

An Soki Ganduje kan Kalamai Mabambanta game da Sahihancin Sarautar Sanusi II

  • Gogaggen masanin tarihi da al’adun Arewa, Ibrahim Ado Kurawa, ya caccaki tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Kurawa ya yi magana ne game da kalamansa mabambanta kan takaddamar masarautar Kano da ya shafi Muhammadu Sanusi II
  • Ya bayyana cewa shari’ar da ke gaban Kotun Koli ba ta shafi taƙaddamar masarautar Kano ba, illa hakkokin Aminu Babba DanAgundi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Masani kan al’adun Arewa kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, Ibrahim Ado Kurawa ya soki Abdullahi Ganduje kan kalamansa.

Kurawa ya zargi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da yin kalamai masu cin karo da juna dangane da rikicin masarautar Kano.

An soki Ganduje kan kalamansa game da Sanusi II
Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje (hagu) da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (dama). Hoto: Ganduje TV, Sanusi Lamido Sanusi.
Source: Facebook

Ibrahim Kurawa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai kan shari’ar da ke ci gaba da gudana a kotu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta ƙare ba: kotu ta ɗage shari'ar rikicin shugabancin ADC a Abuja

Ana zargin ƴan siyasa da juya rikicin masarauta

Kurawa ya ce wasu ‘yan siyasa suna kokarin juya rikicin zuwa takaddamar sarauta, alhali shari’ar da ke gaban Kotun Koli ba ta shafi wanda yake kan karagar sarautar Kano ba.

Ya bayyana cewa karar da aka shigar ta fito ne daga wani mai sarauta wanda yake zargin soke dokar masarautun Kano ya tauye masa hakkokinsa na asali.

A cewarsa, lauyoyin gwamnati da na Aminu Babba DanAgundi sun tabbatar bayan zaman kotu cewa batun da ake dubawa ya shafi hurumin kotu da hakkokin dan adam ne kawai.

Kurawa ya jaddada cewa rikicin bai shafi halaccin Muhammadu Sanusi II ko Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano ba.

Ya soki Ganduje kan abin da ya kira rashin daidaito a matsayinsa, yana mai tunatar da shi yadda ya taba kiran Sanusi II a matsayin Sarki yayin rantsar da Murtala Sule Garo a gidan gwamnati.

Ganduje ya gyara maganarsa kan sahihancin sarautar Sanusi II
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Rikicin masarauta: Kurawa ya caccaki Ganduje

Kara karanta wannan

Abba ya yi tattaki zuwa Abuja, ya mika fam neman takarar gwamnan Kano

Daga baya, Ganduje ya bayyana ta bakin tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammad Garba, cewa ya yi hakan ne saboda ladabi da ka’ida kawai.

Sai dai Kurawa ya tambayi dalilin da ya sa Ganduje ya kai dan uwansa wajen Muhammadu Sanusi II domin nada shi sarautar shugaban kauyen Ganduje idan har bai amince da shi a matsayin Sarki ba.

Ya kuma tuna da dokar masarautun Kano ta shekarar 2019 da gwamnatin Ganduje ta kirkiro sababbin masarautu a karkashinta, cewar The Guardian.

Kurawa ya ce yana cikin wadanda suka kalubalanci dokar tare da marigayi Bashir Tofa da wasu mutane saboda kura-kuran tsarin amincewa da ita.

Ya bayyana cewa duk da kotu ta soke dokar, Ganduje bai tube sarakunan da aka nada ba, sai dai ya sake gabatar da dokar ga majalisar dokokin Kano domin gyara matsalolin tsarin da aka nuna.

Sanusi II ya soki cin bashin Tinubu

An ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kalubalanci gwamnatin tarayya bayan cire tallafin mai a Najeriya wanda ya jawo maganganu a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta kashe mutane bayan nada Murtala Garo, ta soki Amnesty

Sarkin ya tambayi dalilin ci gaba da karbar bashi duk da cire tallafin mai, yana gargadin cewa rashin daidaito na iya lalata ribar sauye-sauyen.

Ya ce gyaran farashin dala da cire tallafi sun dace amma lokaci da rashin tsauraran manufofi sun janyo faduwar Naira, yana bukatar karin tsari mai kyau.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.