An Fara Kokarin Jawo Hankalin Yan Arewa domin Su Zabi Peter Obi da Kwankwaso a 2027

An Fara Kokarin Jawo Hankalin Yan Arewa domin Su Zabi Peter Obi da Kwankwaso a 2027

  • Kungiyar OKICAN ta jaddada goyon bayanta ga tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a zaben shugaban kasa na 2027
  • Ta kuma ayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NDC, Kwamared Abdulsalam Gwarzo
  • Kungiyar na shirin kafa rassa a kananan hukumomi 44 da unguwanni 484 na Kano, kuma za ta fadada ayyukanta zuwa jihohi 19 na Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kungiyar Obi-Kwankwaso Inter-Community Alliance Network (OKICAN) ta fara aikin tallata tikitin takarar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga Obi da Kwankwaso, wadand za su fafata da sauran yan takara karkashin inuwar jam'iyyar NDC a zaben 2027 mai zuwa.

Obi Kwankwaso.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi tre da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta kuma ayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan Kano na NDC, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, tare da sauran 'yan takarar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Rarara ya kira ruwa, PDP ta yi masa tatas kan taba Farfesa Pantami

Za a fadada kungiyar a Kano da Arewa

A wata sanarwa da jagoran kungiyar na kasa, Hon. Tableth Onuoha, ya sanya wa hannu, OKICAN ta ce tana hada al'ummomin da ba 'yan asalin Kano ba a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar domin gina karfin siyasa.

Onuoha, wanda tsohon kansila ne a Kano kuma tsohon mai rike da mukami a gwamnatin tarayya, ya ce kungiyar za ta fadada irin wannan tsari zuwa dukkan jihohi 19 na Arewacin Najeriya don tallata Obi/Kwankwaso.

Kano na da muhimmanci a siyasar Arewa

A cewarsa, Kano na da muhimmanci matuka saboda yawan mutanen da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya da ke zaune a jihar.

Ya ce:

"Kano ita ce cibiyar siyasa da kasuwanci ta Arewacin Najeriya, kuma tana dauke da sama da mutane miliyan 2.5 da ba 'yan asalin jihar ba, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci, masana'antu da ci gaban al'umma."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Ya kara da cewa al'ummomin Igbo, Yarabawa, Edo, Delta, Ijaw, Idoma, Igala, Tiv, Ibibio, Nupe da sauran kabilun Kudancin Najeriya da yankin Middle Belt na cikin wadanda ake hada su cikin wannan shiri.

NDC .
Tutar jam'iyyar adwa ta NDC a Najeriya Hoto: NDC Party
Source: Facebook

Ta bukaci hadin kan shugabannin al'umma

A matsayin wani bangare na shirinta, OKICAN ta ce za ta hada kai da sarakunan gargajiya, kungiyoyin kasuwanni da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kuma karfafa shiga zabe cikin lumana.

Kungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin al'ummomi da kungiyoyin kabilu da ke zaune a Arewacin Najeriya da su shiga cikinta yayin da take ci gaba da fadada tsarinta a yankin, in ji rahoton Daily Post.

Kungiyar OK Movement ta fada rikici

Kun ji cewa rikicin cikin gida ya ɓarke a ƙungiyar OK Movement mai goyon bayan takarar tsohon gwamna Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso a 2027.

Bangarori daban-daban da ke ikirarin shugabancin ƙungiyar sun fara musayar zarge-zarge a bainar jama'a duk da rokon da Peter Obi ya yi.

Matsalar ta fara ne bayan wata sanarwa da Jackie Wayas ta fitar, inda ta bayyana kanta a matsayin jagorar ƙungiyar ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262