China Ta Dauki Mataki kan Amurka bayan Gano Makamansu Sun Ragu a Yakin Iran

China Ta Dauki Mataki kan Amurka bayan Gano Makamansu Sun Ragu a Yakin Iran

  • China ta sanar da sababbin takunkumai kan wasu kamfanonin Amurka tare da tsaurara dokar fitar da jiragen sama marasa matuƙa zuwa Amurka
  • Beijing ta ce matakin martani ne ga takunkuman da Washington ta kakaba wa kamfanonin China kan zargin take haƙƙin ɗan Adam
  • Sababbin matakan sun zo ne gabanin taron da ake sa ran shugabannin China da Amurka, Xi Jinping da Donald Trump, za su yi a watan gobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Beijing, China – Gwamnatin China ta sanar da kakaba sababbin takunkumai kan wasu kamfanonin Amurka tare da ƙara tsaurara dokokin fitar da jiragen sama marasa matuƙa da kayan da ake amfani da su zuwa Amurka.

China ta bayyana cewa matakin martani ne ga jerin takunkuman da gwamnatin Amurka ta ɗauka kwanan nan kan kamfanonin China da sauran matakan kasuwanci.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya

Xi Jinping da Donald Trump
Xi Jinping a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta rahoto cewa wannan na zuwa ne gabanin taron da ake sa ran shugaban China Xi Jinping da shugaban Amurka Donald Trump za su yi a Amurka a watan Satumban 2026.

Dalilin da China ta ɗauki matakin

Ma'aikatar kasuwancin China ta ce ta sanya kamfanonin Amurka guda bakwai cikin jerin takunkumi, inda ta hana kamfanoni da mutane a cikin China yin hulɗa da su.

A cewar ma'aikatar, kamfanoni shida sun shiga jerin ne saboda matakin Amurka na haramta shigo da kayayyaki daga kamfanonin China 43 bisa zargin take haƙƙin ƴan kabilar Uyghur da sauran tsiraru.

An kuma ɗaura kamfani na bakwai cikin jerin bayan Hukumar Sadarwa ta Amurka (FCC) ta haramta shigo da sababbbin mutummutumin robot da wasu na'urorin lantarki da ake ƙerawa a China.

Euro News ta ce China ta kuma sanar da fara binciken tsaron ƙasa kan wasu kayan ofis da ake shigo da su masu amfani da manhajojin ƙasashen waje, tare da dakatar da wasu shirye-shiryen haɗin gwiwa da Amurka.

Kara karanta wannan

Amurka ta lissafa Najeriya da wasu kasashen Afrika dake fuskantar barazanar tsaro

China ta yi gargaɗi ga Amurka

Kakakin ma'aikatar kasuwancin China ya ce Beijing ba ta da wani zaɓi face ɗaukar matakan ramuwar gayya domin kare muradunta.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka ta janye takunkuman da ta kakaba wa kamfanonin China tare da dakatar da matakan da zai iya dagula dangantakar ƙasashen biyu.

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump zai ziyarci China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kakakin ya ƙara da cewa idan Amurka ta ci gaba da kakaba sababbbin takunkumai kan China, Beijing za ta ɗauki ƙarin matakan martani.

Ana karancin makami a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa rahotanni sun nuna rundunar sojin Amurka ta yi amfani da kusan dukkan manyan makamai masu linzami na dogon zango da take da su yayin yaƙin da ta yi da Iran.

An bayyana cewa makaman ATACMS da (PrSM), waɗanda suke cikin muhimman makaman rundunar, sun ragu matuƙa bayan watanni ana amfani da su.

Rahotannin sun ce wannan na iya tilasta wa gwamnatin Donald Trump komawa amfani da jiragen yaƙi masu matuƙa idan ta sake ƙaddamar da manyan hare-hare kan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng