Aminu/Sanusi II: An Fayyace Waɗanda Dan Agundi ke Shari'a da Su a Rikicin Masarautar Kano

Aminu/Sanusi II: An Fayyace Waɗanda Dan Agundi ke Shari'a da Su a Rikicin Masarautar Kano

  • Wani Lauya ya bayyana cewa shari’ar Aminu Babba Dan’agundi a Kotun Koli ba ta shafi rikicin sarautar Kano ba da ake ciki
  • Lauyan ya ce Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ba su cikin karar, domin shari’ar tana tsakanin Dan’agundi da gwamnatin Kano
  • Kotun ta dage sauraron karar zuwa Afrilu 2027 bayan an nemi karin lokaci, duk da adawar lauya, domin tabbatar da adalci a shari’ar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani lauya da ke cikin rikicin shari’ar masarautar Kano, Bashir Muhammad Tudun Wizirci, ya yi karin haske kan rikicin sarautar.

Lauyan ya bayyana cewa karar da ke gaban Kotun Koli ba ta shafi sauya ko dawo da wani Sarki ba daga cikin sarakunan biyu.

Lauya ya ce ya yi karin haske kan shari'ar sarautar Kano
Aminu Ado Bayero, Gwamna Abba Kabir da Sanusi II yayin taro a Kano. Hoto: Masarautar Kano, Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Twitter

Wadanda karar Dan Agundi ta shafa a Kano

Kara karanta wannan

Amurka za ta jefa Iran a sabuwar matsala, fada ya koma kan gasar cin kofin duniya

Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotu, Wizirci ya ce karar da Aminu Babba Dan’agundi ya shigar tana tsakaninsa da gwamnatin Kano kawai, ba tare da wani basarake ba, cewar Tribune.

Ya jaddada cewa mutane irin su Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ba su cikin karar, yana mai cewa shari’ar tana tsakanin Dan’agundi da gwamnati da hukumomin tsaro.

“Ina tabbatar da cewa babu sunan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ko tsohon Sarki Aminu Ado Bayero a cikin wannan shari’a, tana tsakanin Dan’agundi da gwamnati.'

- In ji Lauya Wazirci

Ya kara da cewa wadanda aka jera a matsayin masu kare kansu sun hada da majalisar dokokin Kano, ofishin Antoni Janar, da kuma hukumomin tsaro daban-daban.

Kotu ta dage shari'ar sarautar Kano zuwa 2027
Taswirar jihar Kano da rikicin masarauta ya dauki hankulan yan Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Lauyan Dan Agundi ya yi martani

Lauyan Aminu Babba Dan’agundi, Mamman Lawal Yusufari, shi ma ya tabbatar da cewa shari’ar ta takaita ne ga bangarorin biyu, ya kuma karyata alaka da rikicin sarautar Kano.

Wizirci ya bayyana cewa shari’ar ta fara ne a Babbar Kotun Tarayya, amma Kotun Daukaka Kara ta soke ta bisa rashin hurumin kotun, wanda ya sa aka kai karar Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Manyan 'yan siyasa sun raka Yusuf Buhari wajen gwamna Radda

Ya ce duk da an tsara sauraron karar, ba a ci gaba ba saboda wata sabuwar bukata daga bangaren mai kara, da ya ce ya samu jinkirin bayani daga DSS, cewar Leadership.

Duk da adawar da aka yi, kotun ta amince da bukatar karin lokaci domin tabbatar da adalci, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2027.

Yusufari ya kuma bayyana cewa an shirya sauraron karar ne ba yanke hukunci ba, yana mai cewa akwai wata bukata da ke bukatar a mayar da martani cikin kwanaki 14.

An danganta wannan shari’a da wata doka ta 2024 da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu, wadda ta jawo tsige wasu sarakuna da dawo da Sanusi II.

Dan’agundi ya kalubalanci dokar, yana mai cewa ta tauye masa hakkinsa, wanda hakan ya kai ga rikicin shari’a da ake ci gaba da sauraro a Kotun Koli yanzu.

Abba Kabir ya tabo batun sarautar Kano

A baya, an ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce addu'o'in neman hadin kai da zaman lafiya tsakanin jagororin siyasar Kano sun fara haifar da sakamako.

Kara karanta wannan

Atiku da Kwankwaso na tsaka mai wuya, Kotun Koli ta zo matakin karshe kan rikicin ADC

Abba Gida-Gida ya sake jaddada cewa nan ba da jimawa ba, za a warware rikicin sarautar Kano ta hanyar da kowame bangare zai gamsu.

Mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bukaci sauran jihohi da su yi koyi da Kano wajen shirya tarukan addu'o'i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.