Gwamnatin Tinubu Ta Sauko bayan 'Yan Katolika Sun Ja Daga, Za a Tattauna
- Gwamnatin Tarayya ta yi magana bayan limaman Katolika a Najeriya sun ja zare da ita game da batun inganta rayuwar talakawa da habaka tattalin arziki
- Bayan an jima ana musayar zance tsakanin bangarorin biyu, yanzu gwamnatin ta ce za ta zurfafa haɗin gwiwa da limaman Katolika
- George Akume, sakataren gwamnatin Tinubu ya ce Shugaban kasa yana maraba da shawarwari na gaskiya daga shugabannin addini da sauran ƙungiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da limaman Katolika na Najeriya (CBCN), ƙungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki domin fuskantar matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan muhawarar da ta biyo bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da shugabannin CBCN a makon da ya gabata.

Source: Facebook
Daily Trust ta kawo labarin cewa yayin taron, limaman Katolika sun bayyana damuwarsu kan ƙaruwar rashin tsaro, matsin tattalin arziki, yanayin dimokuraɗiyya da yadda ake gudanar da zaɓe a Najeriya.
Abin da ya hada Tinubu da yan Katolika
Daily Post ta wallaaf cewa bayan taron, Archbishop na Cocin Katolika na Abuja mai ritaya, Cardinal John Onaiyekan, wanda ya halarci ganawar, ya bayyana cewa Tinubu ya gana da su kuma sun fadi matsalar da kasa ke ciki.
Sai dai kakakin shugaban ƙasa guda biyu, Temitope Ajayi da Daniel Bwala, sun soki kalaman Onaiyekan, suna cewa bai dace ya fito fili yana bayyana yadda ya fahimci abin da ya faru a taron sirrin da aka yi da shugaban ƙasa ba.
Martanin nasu ya jawo suka daga wasu masu sharhi, inda da dama suka goyi bayan Onaiyekan da sauran limaman Katolika, suna cewa sun faɗi gaskiya ga masu mulki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Yomi Odunuga, ya fitar, Akume ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da tuntubar limaman Katolika da sauran masu ruwa da tsaki kan batutuwan da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya.
Gwamnatin Tinubu na maraba da shawari - Akume
Ya ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta ba za a iya magance su ba sai da haɗin gwiwar ƙungiyoyin addini, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula, kamfanoni masu zaman kansu da kuma al'umma baki ɗaya.
Akume ya bayyana tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba Tinubu da limaman a matsayin wadda ta kasance cikin gaskiya, girmamawa da fahimtar juna, inda aka tattauna batutuwan tsaro da matsin rayuwa.

Source: Facebook
Sauran abubuwan da aka tattauna sun hada da samar da ayyukan gwamnati, ilimi, sahihancin zaɓe, dimokuraɗiyyar jam'iyyu da kuma 'yancin addini.
Ya ce duk da cewa gwamnati da Cocin Katolika na iya samun sabanin ra'ayi kan wasu batutuwa, hakan bai kamata ya hana su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya ba.
Tinubu ya farantawa sojoji
A baya, kun samu labarin cewa wasu dakarun Sojojin Najeriya sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karin albashi da ya yi musu daga kashi 30 zuwa 80 bayan matakin da shugaban kasar ya dauka.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa sojoji karin albashi domin inganta walwalarsu musamman bayan bayanai sun fito cewa ana biyan dakarun N100,000 a wata duk da namijin kokarin da suke yi wa Najeriya.
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da abin da ya kira karin albashi mai cike da tarihi ga jami'an rundunar sojin Najeriya.
Asali: Legit.ng


