Bayan Ambatar Sunan Minista, Wani Dan Kasuwa Ya bada Bayani kan Shirin Yiwa Tinubu Juyin Mulki

Bayan Ambatar Sunan Minista, Wani Dan Kasuwa Ya bada Bayani kan Shirin Yiwa Tinubu Juyin Mulki

  • Wani dillalin motoci ya shaida wa masu bincike cewa Kanal Mohammed Ma’aji ya sayi motoci shida kan Naira miliyan 65
  • Ana zargin an sayi motocin ne a watan Satumban 2025, lokacin da ake kyautata zaton masu shirin juyin mulki sun tsananta shirye-shiryensu
  • Rahotannin bincike sun nuna cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da gurfanar da mutane shida kan zargin kitsa juyin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani dillalin motoci da ke Abuja ya shaida wa masu bincike cewa wani jami'in rundunar soji da ake zargi da jagorantar shirin juyin mulki a 2025 ya sayi motoci shida kan kudin Naira miliyan 65.

Wannan na zuwa ne yayin da rahoton binciken da aka yi zargin yunkurin hambarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke kara fitowa.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya yi barazana ga Tinubu, zai yi murabus daga jam'iyya mai mulki

Kanal Maaji.
Wanda ake zargi da jagorantar shirin juyin mulki, Kanal Muhammed Ma'aji Hoto: @trendingblog247
Source: Twitter

Rahoton binciken da Premium Times ta samu ya nuna cewa motocin sun hada da motocin Toyota Hilux guda uku, Toyota Prado guda daya da kuma Toyota Corolla guda biyu.

Masu bincike na ganin an sayi motocin ne a watan Satumban shekarar da ta gabata, lokacin da suke zargin masu shirin juyin mulki sun tsananta shirye-shiryensu.

Yadda aka gudanar da cinikin

Shugaban kamfanin Arun G Motors da ke Lokogoma a Abuja, Ahmed Abdulganiyu, ya bayyana wa masu bincike cewa cinikin ya fara ne bayan wani mutum mai suna Aliyu ya tuntube shi domin neman sayen Toyota Corolla.

A cewarsa, daga baya Aliyu ya zo tare da Kanal Mohammed Ma’aji, inda suka nemi ya raka su wasu wuraren sayar da motoci domin nemo motocin da suke bukata.

An biya N65m cikin kashi biyu

Ahmed Abdulganiyu ya ce a ranar 27 ga Satumba, 2025, an tura masa Naira miliyan 46.5 zuwa asusun bankinsa na Access Bank.

Kara karanta wannan

Sunan Minista ya fito a jerin wadanda aka tsara neman tallafinsu don yiwa Tinubu juyin mulki

Ya kara da cewa washegari aka sake tura Naira miliyan 18.5 zuwa asusun wani abokinsa, Christopher Elube, wanda ya ba Kanal Ma’aji bayanan asusun.

Dillalin ya ce bayan an kammala biyan kudin, wani mutum ya zo ya kwashe motocin Toyota Hilux guda uku da Toyota Prado guda daya.

Sai dai ya ce motocin Toyota Corolla guda biyu sun ci gaba da kasancewa a wajen kamfaninsa har zuwa lokacin da ya ba da shaida.

Ya ce:

"Har yanzu ba a zo an kwashe motocin Toyota Corolla guda biyun ba."
Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa da ke fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ana ci gaba da shari'ar zargin juyin mulki

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta gurfanar da mutane shida a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin kitsa juyin mulki domin hambarar da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Haka kuma, wasu jami'an soja masu aiki na fuskantar shari'a a gaban Kotun Soji, inda dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su.

Sunan minista ya fito a shirin juyin mulki

Kun ji cewa wani tsohon kyaftin din ruwa da ake tuhuma kan zargin shirin juyin mulki ya ce ya san da shirin amma bai goyi bayansa ba.

Wanda ake zargin ya bayyana sunan ministan Tinubu sa aka tsara za a nemi talafin kudi daga wurinsa don kifar da shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262