Abba Ya Yi Tattaki zuwa Abuja, Ya Mika Fam na Neman Takarar Gwamnan Kano

Abba Ya Yi Tattaki zuwa Abuja, Ya Mika Fam na Neman Takarar Gwamnan Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa takardar tsayawa takarar gwamna ta 2027 ga uwar jam'iyya mai mulki ta APC
  • Manyan jagororin Kano daga ciki har da Sanata Ibrahim Shekarau da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin sun raka shi
  • Gwamnan ya yi alƙawarin ƙara zuba jari a tituna, ilimi, lafiya da bunƙasa karkara kamar yadda ya fara ayyukan samar da ci gaban Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa takardar tsayawa takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027 ga Kwamitin Ayyuka na Ƙasa na jam’iyyar APC.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta kashe mutane bayan nada Murtala Garo, ta soki Amnesty

Gwamna Kano ya kai fam Abuja
Kawu Sumaila, Gwamna Abba Kabir Yusuf, Malam Ibrahim Shekarau da wasu manyan APC a Abuja Hoto: Sanusi Bature D Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Gwamna Abba ya isa wajen miƙa fam ɗin tare da rakiyar manyan jagororin siyasa daga Kano.

An raka Abba kai fam Abuja

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa daga cikin wadanda suka raka gwamnan har da Sanata Ibrahim Shekarau, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, Sanata Kawu Sumaila, ‘yan majalisar wakilai da sauran fitattun mutane.

Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan miƙa fam ɗin, gwamnan ya bayyana cewa ayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu kira ne da zai zama kara hidimtawa mutanen Kano.

Gwamnan Kano ya yi alkawarin kara inganta Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin wani taro a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya ce gwamnatinsa za ta ƙara faɗaɗa ayyukan bunƙasa birane a faɗin jihar, musamman gine-ginen tituna, faɗaɗa magudanan ruwa da kuma gyaran kasuwanni.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a ƙara mayar da hankali wajen inganta rayuwar jama’a da samar da ci gaba mai ɗorewa ga mazauna jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Gawuna ya bi sahun Kwankwaso, ya bayyana dalilinsa na barin ADC

Gwamnan ya yi alƙawarin ƙara bunƙasa karkara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa bunƙasa yankunan karkara zai ci gaba da kasancewa cikin manyan manufofin gwamnatinsa.

Ya yi alƙawarin ƙara saka hannun jari wajen gina hanyoyin karkara, samar da ruwan sha, inganta cibiyoyin lafiya da kuma makarantu a ƙauyuka.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa za ta ƙara tallafawa harkar noma da shirye-shiryen ƙarfafa matasa da manoma domin samar da ayyukan yi da rage matsalar rashin aikin yi.

A cewarsa, ci gaban matasa da samar masu da damar dogaro da kai zai ci gaba da kasancewa a sahun gaba cikin manufofin gwamnatinsa.

Haka kuma, ya sake jaddada kudirinsa na inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya domin tabbatar da jama’a sun samu ingantattun ayyuka.

Har ila yau, gwamnan ya sake nuna goyon bayansa ga manufofin “Renewed Hope Agenda” domin jawo ƙarin ayyukan gwamnatin tarayya da damammaki zuwa jihar Kano.

Kara karanta wannan

Murtala Garo ya yi aikin farko a matsayin mataimakin gwamnan Kano

Ya gode wa al’ummar Kano bisa ci gaba da nuna masa goyon baya da yarda, yana mai tabbatar masu da ƙarin jajircewa a kan shugabanci na gaskiya da kuma gudanar da mulki mai mayar da hankali kan buƙatun jama’a.

Gwamnatin Kano ta musanta kashe matasa

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan rahotannin da ke cewa an kashe mutane biyar bayan rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta batun tare da yin kakkausar suka kan kungiyar Amnesty International kan rahoton da ta fitar kan zargin kisan matasan.

Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa gwamnatin Kano na matukar kokari wajen shawo kan ayyukan daba da dawo da zaman lafiya a jihar yayin da ake kokarin inganta rayuwar matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng