A Karon Farko, Ganduje Ya Amince da Muhammadu Sanusi II a Matsayin Sarkin Kano

A Karon Farko, Ganduje Ya Amince da Muhammadu Sanusi II a Matsayin Sarkin Kano

  • A wani mataki mai cike da mamaki, tsohon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
  • Ganduje ya kira Sanusi II matsayin sarki kuma shugaban majalisar sarakunan Kano a yayin taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar
  • A cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, mutanen da suka halarci wannan taro, sun kaure da shewa lokacin da Ganduje ya yi furucin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - A karon farko, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Wannan furuci ya faru ne a yayin taron rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

Abdullahi Ganduje ya kira Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Tsohon gwamna Abdullahi Ganduje (hagu) da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (dama). Hoto: Ganduje TV, Sanusi Lamido Sanusi
Source: Facebook

Takaddamar shari'ar masarautar Kano

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito a shafinta na Facebook cewa mahalarta taron, sun kaure da tafi a lokacin da Ganduje ke gaishe da Sarki Sanusi II tare da kiran sa da "shugaban majalisar sarakunan jihar Kano".

Kara karanta wannan

An rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano

A shekarar 2020 ne dai, Ganduje ya sauke Sarki Sanusi II daga Sarautar Kano inda daga bisa ni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da shi bayan lashe zaɓen 2023.

Sai dai, har kawo wannan shekara ta 2026, ana ci gaba da tafka shari'a game da da masarautar Kano tsakanin bangaren Aminu Ado Bayero (da Ganduje ya nada) da gwamnatin Kano.

Legit Hausa ta rahoto cewa Kotun koli ta sanya ranar 19 ga Afrilun 2027 a matsayin sabuwar ranar cigaba da sauraron shari'ar da aka shigar gabanta game da masarautar Kano.

Ta sanya ranar ne domin sauraro tare da karɓar martanin masu ƙara a shari'ar wadda Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar gabanta.

Ganduje ya kira Sanusi II 'Sarkin Kano'

Yayin da ake wannan dambarwar shari'a, kwatsam a yau Talata, sai aka ji Ganduje ya kira Sanusi II a matsayin 'Sarkin Kano' kuma shugaban majalisar sarakunan jihar.

A cikin wani bidiyo da ALameen Ibrahim Hotoro ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ji Ganduje ya na cewa:

"Mai martaba sarkin Kano, kuma shugaban majalisar sarakuna, da sauran muhimman baki..."

Kara karanta wannan

Bayan Pantami, Goje da Sanata Alkali sun yi watsi da 'yan takarar APC a Gombe

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ne karon farko da Ganduje ya fito fili ya amince da Sanusi II a matsayin sarkin Kano tun bayan 'raba garin' da suka yi.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Martanin da mutane suka yi

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutanen Facebook kan wannan lamari:

Har yanzu ana kan shari'ar masarautar Kano tsakanin tsagin Aminu Ado Bayero da Sanusi II.
Aminu Ado Bayero (hagu) da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (dama). Hoto: @masarautarkano, @Imranmuhdz
Source: Twitter

Sadeeq Bappah Garkuwa:

"Ga irin abin da muke ta fada wa Aminu Ado, 'yan siyasa za su kai shi su baro shi, gashi kuma an yi."

Yusuf Suleiman Gaya:

"Kano kenan, ko da me ka zo mun fi ka.
"Gawuna a wajen Kwankwaso, Garo mataimakin Abba Gida Gida
"Kullum kara koya mana karatu ake a filin Allah, Allah ya ba mu ikon ganewa da kuma amfani da karatun da ake koyana mana."

Nu'uman Sulaiman:

"Yin bayani ba ya nufin amince wa dashi a matsayin sarki, kawai ya bi tsarin furotakwal ne ya fadi sunayen mutanen da suke a bangaren manyan baki."

A'isha Dogara Adamu:

"Ai dole ya kira shi da sarki, tunda kotu ta tabbatar da shi a sarkin, kana kuma ba'a kammala da Kotun Allah ya isa ba."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar rikicin sarautar Kano zuwa bayan zaben 2027

Tijjani Saad:

"Ya matsayin Ale Aminu kenan?"

Garo: An rantsar mataimakin gwamnan Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf ya rantsar da Mutala Sule Garo a matsayin mataimkin gwamna a wani taro da aka shirya yau Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.

Tsohon shugaban APC na kasa, kuma tsohon gwamna, Dr. Abdullahi Ganduje da Malam Ibrahim Shekaru na cikin manyan bakin da suka halarci bikin rantsar da Garo.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ta tantance . Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com