El Sayed: Mataimakin Trump Ya Yi Maganar Musulmi Ya Zama Shugaban Amurka
- Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce ba ya fatan Abdulrahman El-Sayed ya zama shugaban ƙasa a nan gaba
- Vance ya yi zargin cewa masu kuɗi da masu ra'ayin mazan jiya ne suka taimaka wa El-Sayed ya lashe zaɓen fidda gwani a Michigan
- El-Sayed dai ya samu tikitin jam'iyyar Democrat bayan nasara a zaɓen fitar gwani, kuma zai fafata a babban zaɓen Sanata na watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC, Amurka – Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa yana fatan Abdulrahman El-Sayed ba zai zama shugaban ƙasar ba a nan gaba.
Vance ya yi wannan furuci ne yayin da yake magana kan muhimmancin kare manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Donald Trump daga duk wata gwamnati da za ta biyo baya.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Source: Getty Images
The Hill ta rahoto cewa kalaman nasa sun zo ne bayan El-Sayed ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Democrat domin neman kujerar Sanata a jihar Michigan.
JD Vance ya soki El-Sayed
Da yake magana a wata hira da Fox News, Vance ya ce:
"Ba ma son gwamnati ta gaba, ko wacece kuwa. Allah Ya kiyaye Abdulrahman El-Sayed ya zama shugaban ƙasa cikin shekara uku. Ba ma son ya rushe duk manyan nasarorin da muka samu."
Vance ya kuma yi zargin cewa nasarar El-Sayed ba ta samo asali daga goyon bayan ma'aikata ba, sai dai daga masu kuɗi da fararen fata masu ra'ayin mazan jiya.
Ya ce El-Sayed yana bayyana kansa a matsayin mai kare talakawa, amma manufofinsa za su iya cutar da masana'antar kera motoci ta Michigan.
Zarge-zarge kan manufofin El-Sayed
Mataimakin shugaban Amurka ya kuma soki ra'ayoyin El-Sayed kan harkokin shige da fice da kasuwanci. A cewarsa, manufofin ɗan takarar Democrat ba su dace da muradun ma'aikatan jihar Michigan ba.
Vance ya yi zargin cewa jam'iyyar Democrat na ƙara karkata zuwa bangaren masu tsattsauran ra'ayi, yana mai cewa irin waɗannan 'yan takara sun fi samun goyon bayan masu ilimi da masu kuɗi.
Ya kuma danganta hakan da rashin gamsuwar wasu matasa da suka kammala jami'a amma suka samu kansu cikin bashi da matsalolin tattalin arziki.
Wanene Abdulrahman El-Sayed?
Abdulrahman El-Sayed likita ne kuma ƙwararre a fannin kiwon lafiya, iyayen shi 'yan Masar ne da suka yi hijira zuwa Amurka.
Ya taɓa zama babban daraktan sashen lafiya na birnin Detroit, sannan ya tsaya takarar gwamnan Michigan a shekarar 2018.

Source: Getty Images
El-Sayed ya yi karatu a Jami'ar Michigan, Jami'ar Oxford da kuma Jami'ar Columbia, kuma yanzu shi ne ɗan takarar jam'iyyar Democrat a zaɓen Sanatan Michigan.
Trump ya soki El-Sayed
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Abdul El-Sayed bayan nasararsa a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar Democrat.
Trump ya kira El-Sayed da sunaye masu zafi, tare da yin zargin ba tare da gabatar da hujja ba cewa ana tafka maguɗin zaɓe a gundumar Wayne da ke jihar Michigan.
Iyanen Abdul El-Sayed 'yan asalin kasar Masar ne da suka koma zama a kasar Amurka kuma yana aiki a matsayin jami'in lafiya kafin ya tsunduma harkokin siyasa.
Asali: Legit.ng
