Janar Abdulsalam Ya Faɗi Abin da ba a Sani ba kan Mutuwar Fuju'a da Abiola Ya Yi
- Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya kawo wasu karin bayanai game da mutuwar MKO Abiola a Najeriya
- Abdulsalam ya ce ba a ba tawagar Amurka damar ganin Abiola ba da farko, amma ya ba da umarnin a kai su wajensa
- Ya bayyana cewa Abiola ya fara tari da zufa yayin ganawa da tawagar kafin daga bisani ya rasu, lamarin da ya girgiza kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana a cikin tarihin rayuwarsa kan mutuwar MKO Abiola.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa jami'an Amurka da suka zo Najeriya domin ganawa da MKO Abiola an hana su ganinsa da farko.

Source: Getty Images
Musabbabin mutuwar MKO Abiola
A cewar bayanan da aka bayar, Abiola ya fara tari ba tsammani sannan daga baya ya rasu, lamarin da ya jawo tarzoma a Lagos, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
"Suna tare cikin daki"; Tsohon jami'in DSS ya fadi abin da ya kashe Janar Sani Abacha
Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga Yunin 1993 da aka soke, ya gana da wata tawagar mutanen Amurka a Abuja ranar 7 ga Yulin 1998.
An yi ta rade-radin cewa an ba shi shayin da ya kunshi guba daga jami'an Amurka domin rage tari da ya fara yi.
Wata guda kafin haka ne Janar Sani Abacha ya rasu babu zato babu tsammai, bayan ya tsare Abiola tun shekarar 1994.
Abdulsalami ya ce tawagar Amurka ta zo Najeriya domin tantance yanayin siyasar kasar bayan mutuwar Abacha da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Source: Getty Images
Yadda aka hana su Abdulsalam ganin Abiola
A cewar Abdulsalami, sun koka cewa an hana su ganin Abiola duk da cewa wannan ne babban dalilin zuwansu Najeriya.
Ya ce ya yi mamakin hakan domin bai san an hana su ba, inda nan take ya umarci CSO dinsa Abdulrasheed Aliyu ya shirya ganawar.
Bayan kiran waya daga Aliyu, Abdulsalami ya samu labarin cewa Abiola ya mutu bayan ya fara tari da zufa a wajen taron, cewar The Nation.
Abdulsalami ya ce sanar da iyalan Abiola labarin mutuwarsa abu ne mai matukar wahala, inda daya daga cikin 'ya'yansa ta fashe da kuka.
Binciken da aka yi kan mutuwar Abiola
An tattaro kwararrun likitocin binciken gawa daga Amurka, Birtaniya, Najeriya da Canada domin gudanar da binciken cikin gaskiya.
Dr Falomo da wakilan 'Nigerian Medical Association' sun halarci dukkan matakan binciken ba tare da wani boye-boye ba.
Rahoton ya nuna cewa Abiola na fama da matsananciyar cutar zuciya ta dogon lokaci da kuma hawan jini.
An gano jijiyoyin zuciyarsa sun toshe sakamakon taruwar kitse, yayin da zuciyarsa ta kara girma saboda hawan jini.
Sakamakon binciken sinadaran jiki bai nuna wata alamar guba ba, lamarin da ya kawar da zarge-zargen kisa.
Wani likitan Amurka, Dr John Pless, ya ce cutar da ta yi sanadin mutuwar Abiola ta dade a jikinsa tsawon shekaru 10 zuwa 14.
Abdulsalam ya magantu kan dawowar mulkin soja
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya yi magana kan masu neman mulkin soja a Najeriya maimakon dimokuraɗiyya.
Janar Abdulsalami Abubakar ya yi magana ne bayan Najeriya ta kwashe shekaru 25 tana mulkin farar hula duk da ƙalubalen da kasar ke fuskanta.
A daya bangaren, Shugaban majalisar dokokin Najeriya ya ce ƙarfafa jam’iyyun siyasa da adawa mai ma'ana na samar da shugabanci nagari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

