'Ya Fita a Raina': Fubara Ya Magantu kan Yiwuwar Komawa Mulki bayan Sanya Dokar Ta Ɓaci
- Gwamna da aka dakatar na Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa bai damu da komawa ofis ba domin ruhinsa ya riga ya fita
- Fubara ya bayyana hakan ne yayin taron karrama marigayi Edwin Clark, inda ya ce maganganun da wasu suka yi ba na shi ba ne
- Shugaba Tinubu ne ya dakatar da Fubara bayan rikici da ‘yan majalisa, sannan ya nada tsohon hafsan soji a matsayin shugaba na wucin gadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Dakataccen gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan dokar ta-ɓaci a jihar.
Fubara ya ce ba shi da wata matsananciyar bukata ta komawa ofis din gwamnati bayan dakatar da shi da aka yi.

Asali: Instagram
Fubara ya bayyana hakan ne a wajen bikin kade-kade da aka yi don girmama marigayi Edwin Clark a birnin Port Harcourt a ranar Lahadi, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musabbabin Tinubu na dakatar da Fubara a Rivers
Shugaba Tinubu ne ya dakatar da Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, da kuma ‘yan majalisar jihar, bayan sanar da dokar ta baci.
Tinubu ya ce hakan ya biyo bayan hare-haren da wasu gungun ‘yan bindiga suka kai kan bututun mai a lokacin rikicin siyasa a jihar.
Shugaban ya kuma nada tsohon hafsan sojin ruwa, Ibok-Ete Ibas, a matsayin shugaba na wucin gadi a wannan jihar mai arzikin man fetur.
Dokar ta-ɓaci: Fubara ya ce bai damu ba
A yayin taron, Fubara ya ce hankalinsa a kwance yake kuma bai ɗaɗara kansa cewa sai ya dawo mulki ba.
Ya ce:
"Ba ku ga yadda na fi kyau ba? Kuna tunanin ina sha’awar komawa? Ruhina tun tuni ya bar wurin."

Asali: Facebook
Fubara ya magantu kan dokar ta-ɓaci
Gwamnan da ke cikin rikici ya fadi haka ne bayan wasu da suka kira shi “Gwamna” kuma suka soki dakatarwar da aka masa.
Fubara ya nesanta kansa daga kalamansu, inda ya ce ra’ayinsu ne na kansu, kuma hakan ba zai kawo zaman lafiya ba.
Ya kara da cewa:
"Ba komai ne sai da karfi ba, ina so kowa ya mai da hankali, akwai fada da bai kamata a yi ba."
Edwin Clark: Fubara ya ba al'umma shawara
Fubara ya bukaci mahalarta su mai da hankali kan tunawa da Edwin Clark wanda ya rayu yana kare yankin Neja Delta.
Rahotanni sun ruwaito a baya cewa Fubara ya ce 'karfin gaskiya da zaman lafiya da ci gaba za su rinjayi rikicin jihar'.
Tinubu ya roki kotu kan dokar ta-ɓaci
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci kotun koli ta yi watsi da karar gwamnonin PDP da ke kalubalantar dokar ta baci da dakatar da Simi Fubara.
Lauyan gwamnatin Najeriya ya ce kotun koli ba ta da hurumin sauraron karar, domin ba ta shafi rikici tsakanin jihohi da tarayya kai tsaye ba.
Jihohin PDP sun roƙi kotun ta soke dakatarwar da kuma nadin shugaban riko, suna masu cewa matakin ya saba wa kundin tsarin mulki.
Asali: Legit.ng