Gwamnan Bauchi na Shan Suka kan Cewa Karatun Boko Shirme ne
- Dr Kabiru Danladi Lawanti ya caccaki kalaman Gwamna Bala Mohammed da ya kira karatun Boko da "shirme", yana mai cewa hakan zai rage darajar ilimi
- Malamin jami'ar ya bayyana cewa matsalolin Arewa ba yawan masu digiri ba ne, sai dai rashin damammakin samun ilimi mai inganci
- Dr Danladi Lawanti ya ce ya kamata a daina rarrabe karatu da koyon sana’a, domin kowanne yana da rawar da yake takawa a cikin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Dr Kabiru Danladi Lawanti ya koka kan wani sabon salo da ke yaduwa a tsakanin al’umma, inda ake nuna cewa koyon sana’a yafi samun digiri a jami’a muhimmanci.
A cewarsa, wannan fahimta ba wai kawai bata dace ba ce, har ma tana iya hana matasa damar kaiwa kololuwar burinsu.

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Dr Lawanti ya nuna damuwa kan wani bidiyo da ke yawo a intanet, inda Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya siffanta karatun Boko da "shirme".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr Kabiru Danladi Lawanti ya shafe shekaru fiye da 10 ya na karantar da ilmin aikin jarida a Jami'ar Ahmadu Bello a Zariya.
Ko da yake ya ce bai tabbatar da cikakken yanayin da aka yi maganar ba, amma kasancewar gwamna da kuma jagora a Arewa maso Gabas, kalmar ta jawo damuwa.
Lawanti ya ce babban kalubale a Arewa ba yawan masu digiri ba ne, sai dai matsalolin rashin tsaro, talauci, da kuma gurbatattun cibiyoyin gwamnati da ke hana yara zuwa makaranta.
Za a iya hada karatun Boko da sana'a
A cewar Dr Lawanti, batun cewa dole mutum ya zabi ko dai sana’a ko kuma karatu ya na da hatsari, domin hakan yana nuna gazawa wajen fahimtar mahimmancin ilimi.
Malamin jami'ar ya ce sana’a ba kishiyar digiri bace, illa kawai karatu hanyar zurfafa koyo da tsari mai inganci ne.
Ya bayar da misalin kansa inda ya ce ya karanta aikin jarida ba don zama mai karanto labarai kawai ba, sai don fahimtar al’umma da amfani da kafar sadarwa wajen gyaran al’umma.

Asali: Facebook
Ya ce wadanda suka kammala wannan fannin na iya aiki a fannonin diplomasiyya, kungiyoyi, kafafen yada labarai na duniya da ma manyan ofisoshin gwamnati.
Dr Lawanti ya fadi haka ne domin a cewarsa tsarin karatun na koya wa mutum dabarun tunani, rubutu da tattaunawa cikin basira.
Ya kamata talaka ya yi karatun Boko?
Dr Kabiru Lawanti ya jaddada cewa fadakar da yaran talakawa da su bar karatu su koma koyon dinki ko gyaran waya ba taimako ba ne, illa rage musu hanyoyin cimma burinsu.
Ya ce yayin da ’ya’yan manya ke samun damar zuwa makarantun duniya, yaran talakawa su ke shan wahala da raunin tsarin ilimi.
Ya bukaci gwamnati da al’umma su sake tunani, su gina tsarin da zai baiwa matasa damar samun ilimi da sana’a.
Gwamnan Bauchi ya raba mukamai
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya ba mutane da suka kusan 200 mukaman siyasa.
Nadin mukaman ya zo ne a daidai lokacin da aka fara ganin hotunan gwamna Bala Muhammad ka shirin takarar shugaba kasa a 2027.
Sai dai Legit ta rahoto cewa wani daga cikin wandanda aka ba mukamin a karamar hukumar Katagum, Musa Azare ya ki karba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng