'Ƙarya ce Tsagwaronta': Kwamishinan Matawalle Ya Yi Martani Mai Zafi ga Gwamna Dauda

'Ƙarya ce Tsagwaronta': Kwamishinan Matawalle Ya Yi Martani Mai Zafi ga Gwamna Dauda

  • Tsohon kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Dosara, ya musanta ikirarin Dauda Lawal cewa N4m kacal ya samu a baitul-mali
  • A cewar Dosara, gwamnatin Bello Matawalle ta bar kudi masu yawa ciki har da N14bn daga tallafin bashi da sauran kudin kasashen waje
  • Dosara ya bayyana cewa Mai girma Dauda Lawal ya zargi gwamnatin baya da laifuffuka ba bisa hujja ba a wata hira da ya yi da yan jaridu
  • Ya kara da cewa an samu bashi na albashin wata uku kacal, saboda sabon gwamna ya hana bankuna hulda da gwamnatin da ta shude

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya yi martani ga ikirarin Gwamna Dauda Lawal.

Dosara ya musanta ikirarin gwamnan cewa ya samu N4m ne kawai lokacin da ya karbi ragamar mulkin jihar.

Tsohon kwamishinan Matawalle ya soki kalaman Gwamna Dauda Lawal
Tsohon kwamishina a mulkin Bello Matawalle ya martani ga Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dr. Bello Matawalle, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Kwamishinan Matawalle ya yi martani ga Dauda Lawal

Dosara ya mayar da martani ne kan wata da Lawal ya yi da ƴan jaridu a ranar 14 ga Afrilun 2025, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kwamishinan a mulkin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ce babu gaskiya cewa Dauda Lawal ya samu jihar a lalace.

Dosara ya bayyana wannan ikirari a matsayin “karya tsagwaron gaske" da bai kamata mutane su amince da ita ba.

A martaninsa, ya ce:

“Mun shiga cikin lamarin ne saboda gwamnatinmu ta karkashin tsohon gwamna Bello Matawalle, ta yi fama da zargi mara tushe daga Gwamna Dauda Lawal."
“Wannan karya ce tsagwaron gaske. Domin tabbatarwa, tsohon gwamna ya bar: N14bn na bashi, N2.6bn daga Bankin Duniya da N6.3bn na tallafin hukumar UBE.”
“Haka kuma akwai N2.7bn daga tallafin 'NG Cares', wanda ya samar da ribar N42bn ga gwamnatin Lawal."
Na jikin Matawalle ya soki ikirarin Dauda Lawal a Zamfara
Tsohon kwamishinan Matawalle ya caccaki Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Akasin da aka samu a mulkin Matawalle

Dosara ya kara da cewa tsohon gwamnan ya bar bashin albashi na wata uku kacal, saboda rashin isasshen kudin shiga da jihar ke samu.

Tsohon kwamishinan ya yi kokwanton zargin Dauda Lawal cewa akwai rabin albashi a tsarin ma'aikatan gwamnati a jihar, cewar rahoton Punch.

Ya kara da cewa:

“Ina kokonto ko akwai rabin albashi a tsarin ma’aikatan gwamnati, tsarin bai kai yadda aka bayyana ba.
“Domin bayyana gaskiya, an samu bashi na wata uku ne saboda tun kafin karbar mulki, Lawal ya hana bankuna hulda da gwamnatin da ta shude.”

Dauda Lawal ya musanta shirin barin PDP

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya karyata jita-jitar barin PDP, yana cewa labaran karya ne da ba su da tushe ko makama.

A wani rubutu da ya wallafa a Facebook, Gwamna Lawal ya bayyana cewa shi cikakken ɗan jam'iyyar PDP ne kuma bai da niyyar canza jam’iyya zuwa wata.

Gwamnan ya ce wasu ke yaɗa jita-jitar domin su ɓata masa suna da kawar hankalin jama'a daga nasarorin da yake samu a Zamfara saboda wata bukata ta karan kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.