Ministan Tsaro, Musa Ya Fallasa Rukunin Mutane 2 da ke Taimakon 'Yan Bindiga a Najeriya

Ministan Tsaro, Musa Ya Fallasa Rukunin Mutane 2 da ke Taimakon 'Yan Bindiga a Najeriya

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce masu taimaka wa ‘yan ta’adda a cikin al’umma ne ke ƙarfafa ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane
  • Janar Musa mai ritaya ya bayyana cewa ‘yan ta’adda na samun abinci, ruwa, bayanan sirri da kayan aiki daga wasu mutane a yankunan karkara
  • Ya yi kira ga ‘yan Najeriya su haɗa kai tare da tona asirin duk masu taimaka wa miyagu, yana mai cewa ta haka ne kadai zaman lafiya zai dawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Tsaro na Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana rukunin mutane biyu da ke kara rura wutar matsalar tsaro kasar nan.

Ya ce masu bada bayanai da ake kira imfoma da masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya ne suka sa matsalar tsaro ta ci gaba da ƙamari a ƙasar.

Kara karanta wannan

Dan bindiga ya kai hari Amurka ana gasar kofin duniya a kasar

Christopher Musa.
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa (mai ritaya) Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa Musa ya bayyana haka ne yayin taron The Platform Nigeria 2026, wanda aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Dimokuraɗiyya.

Ya ce ba zai yiwu a kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba idan har jama’a ba su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai da goyon baya ba.

Yadda mutane ke taimakon yan ta'adda

A cewar ministan, ƙungiyoyin ta’addanci da ‘yan bindiga suna samun damar ci gaba da ayyukansu ne saboda wasu daga cikin jama’a na ba su taimako.

Ya ce suna samun abinci, ruwa, bayanan sirri da sauran kayan aikin da ke taimaka musu wajen gudanar da hare-hare.

“Komai ya ta’allaka ne da jama’a. Idan jama’a sun shirya samun canji, canji zai samu. Idan ba su shirya ba, babu abin da zai canza.
“Akwai mutane da ke ƙarfafa da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci saboda ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suna rayuwa ne a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan

Duniya za ta huta: Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe, babu sauran kai hari

“Su wane ne ke ba su kuɗi? Su wane ne ke ba su bayanai? Su wa ke samar musu da kayan aiki da dabarun gudanar da ayyukansu? Har yanzu mutane ne,” in ji shi.

Matsalar tsaro ta sauya salo

Ministan ya ce yaƙein zamani sun bambanta da na baya, domin a yanzu maƙiyi ba ya bayyana kai tsaye, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

“A baya yaƙi yana tsakanin ƙasa da ƙasa ne, ka san maƙiyinka. Amma yanzu mafi haɗarin yaƙi shi ne lokacin da maƙiyi yake cikin jama’ar da kake karewa.”
Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da jami’an tsaro ke karewa na iya kasancewa su ne ke taimaka wa masu aikata laifuffuka a ɓoye.

Musa ya jaddada cewa duk ƙoƙarin da rundunonin tsaro za su yi ba zai wadatar ba idan jama’a ba su bayar da bayanai da haɗin kai ba.

Tinubu ya aika sako ga yan ta'adda

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa ba za a nuna jin kai ga masu haddasa ta'addanci da masu taimaka masu ba a Najeriya.

Tinubu ya bai wa 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyin ta'addanci wa'adi su mika wuya.

A cewarsa, sama da mayaƙan kungiyoyin yan tada kayar baya da masu dogaro da su 124,000 sun ajiye makamansu tun shekarar 2023 ta shirin Operation Safe Corridor.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262