Bayan Ziyarar Fubara da Rakiyar Gwamnonin APC, Wike Ya Faɗi Raunin Dakataccen Gwamna
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da ziyarar Siminalayi Fubara tare da gwamnoni biyu na APC, yana mai cewa suna kokarin sasanci
- Wike ya ce bai yarda Fubara na da karfin kawo zaman lafiya ba, yana sukar yadda magoya bayansa ke ci gaba da tayar da hankali a jihar Rivers
- Fubara ya bukaci magoya bayansa da su dakatar da daukar matakai da sunansa, yana cewa wasu ayyukan suna barazana ga kokarin sasanci da ya fara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan ganawarsa da Siminalayi Fubara.
Wike ya tabbatar da cewa dakataccen gwamnan Rivers, Fubara, ya kai masa ziyara da rakiyar wasu gwamnonin APC.

Asali: Twitter
Gwamnonin APC sun raka Fubara zama da Wike
Wike ya bayyana hakan ne a hira kai tsaye da manema labarai a ranar Litinin 12 ga watan Mayun 2025, cewar rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan Rivers ya ce ana kokarin warware rikicin siyasa a Jihar Rivers bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci.
Wike ya ce gwamnonin biyu da suka raka Fubara mambobin jam’iyyar APC ne, kuma ba shi da matsala da su ba.
Ya ce:
“Eh, ya zo da gwamnoni biyu da wani mutum, amma gwamnoni biyun na APC ne, don haka ba zan yi musu bita da kulli ba."
“Ya ce yana son zaman lafiya, da kyau, ni ma ina so amma dole ne ya dauki matakan da suka dace."
Tsohon gwamnan Rivers ya nuna rashin yarda da gaskiyar Siminalayi Fubara, yana cewa ayyukansa ba su nuna cewa yana son zaman lafiya ba.
“Na ce masa, ban ga kana da karfin kawo zaman lafiya ba. Idan ka na da niyya, me ya sa ake zanga-zanga kullum?.
“Idan kana da niyyar sasanci, me ya sa magoya bayanka ke zagi a talabijin? Ba kawai da baki ake sasantawa ba."
- Cewar Wike

Asali: Facebook
Wike ya yi fatali da maganganun Fubara
Wike ya mayar da martani ne ga jawabin Siminalayi Fubara a ƙarshen mako, inda ya roki magoya bayansa da su guji kara dagula lamura a halin da ake ciki.
Ya watsar da maganganun Fubara, yana cewa halin da yake ciki yanzu abin da ya jawo wa kansa ne, Punch ta ruwaito.
Ya ce:
“Lokacin da wannan rikici ya fara, na kira shi. Seyi Makinde ya halarta. Ortom, Ikpeazu da Ugwuanyi duk sun kasance a wurin.
"Mun zaunar da shi muka ce, ‘Wannan ba zai amfane ka ba.’ Allah ya baka wannan matsayi ka nuna kankan da kai.
“Su na gaya masa ya zama gwamna. Eh, mun san shi ne gwamna, ba wanda ke kokarin kwace masa, amma ka da yamanta da masu taimakonsa.”
Fubara ya magantu kan dawowa mulki
Kun ji cewa Gwamna da aka dakatar na Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa bai damu da komawa ofis ba domin ruhinsa ya riga ya fita.
Fubara ya bayyana hakan ne yayin taron karrama marigayi Edwin Clark, inda ya ce maganganun da wasu suka yi ba na shi ba ne.
Hakan ya biyo bayan dakatar da shi da Bola Tinubu ne ya yi bayan rikici da ‘yan majalisa da ya dabaibaye jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng