Jerin jihohi 6 da NECO ke bi bashin kudin jarabawa Naira biliyan 1.8

Jerin jihohi 6 da NECO ke bi bashin kudin jarabawa Naira biliyan 1.8

  • Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta ce tana bin jihohi shida bashin Naira biliyan 1.8 na daliban da suka yi wa rajista a shekarar 2019
  • Jihohin sune, Zamfara, Adamawa, Kano, Niger, Borno da Gombe
  • Ta bayyana hakan ne yayinda take bayani kan ragowar da aka samu a kudaden da hukumar ta aike wa gwamnatin tarayya

Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta bayyana jihohi shida da take bi bashin Naira biliyan 1.8 na daliban da suka yi wa rajista a shekarar 2019.

Daraktan Kudi na NECO (DFA), Jacob Ekele, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, lokacin da hukumar ta bayyana a gaban kwamitin bincike a majalisar wakilai kan harkokin kudi, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANNTA KUMA: ‘Yan adaidaita sahu a Kano za su biya N100,000 don samun sabon lasisin tuki - Hukumar KAROTA

Jerin jihohi 6 da NECO ke bi bashin kudin jarabawa Naira biliyan 1.8
Jihar Zamfara ce kan gaba a jerin jihohin da ake bi bashin Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Ga jerin jihohin guda shida a kasa:

1. Zamfara (biliyan N1.2)

2. Adamawa (N281.4 miliyan)

3. Kano (N240.4 miliyan)

4. Niger (N234.4 miliyan)

5. Borno (N40.2 miliyan)

6. Gombe (N7.2 miliyan)

An samu ragowa a kudaden da NECO ta turawa FG

Legit.ng ta tattaro cewa Ekele ne ya kawo batun bashin yayin da yake bayanin dalilin ragowa a cikin kudaden da hukumar ta baiwa gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Jihohi bakwai da suka yi kaurin suna wajen lalacewar hanyoyi a Najeriya — Rahoto

A cewarsa, jihar Zamfara ce kan gaba a jerin jihohin da ake bi bashin da biliyan N1.2, sannan Adamawa na biye da N281.4 miliyan.

Ana bin Kano bashin Naira miliyan 240; Ana bin Neja bashin Naira miliyan 234.4; ana bin Borno Naira miliyan 40.2 yayin da ake bin Gombe Naira miliyan 7.2.

Kashi 90 na ‘yan aji biyar sun fadi jarrabawar kwalifai a Jihar Kano

A wani labarin, mun ji cewa kimanin kashi 90 na daliban da suka rubuta jarrabawar kwalifai a Jihar Kano sun gaza tabuka wani kwazo.

Cin jarrabawar ta kwalifai kan bai wa dalibi damar gwamnatin jihar ta biya masa kudin rubuta babbar jarrabawar kammala sakandare.

Har sai dalibi ya samu sakamako mai kyau wato kiredit a darussa bakwai ciki har da darasin Lissafi da na Turancin Ingilishi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel