Malamin Musulunci Ya Magantu da Zulum Ya Haramta Giya, Ya Taɓo Batun Hisbah a Borno

Malamin Musulunci Ya Magantu da Zulum Ya Haramta Giya, Ya Taɓo Batun Hisbah a Borno

  • Babban limamin Musulunci a jihar Borno ya yaba da haramta sayar da giya da Gwamna Zulum ya yi a lokacin da ya dace
  • Limamin da ke filin jirgin sama na Maiduguri, ya bukaci gwamnati ta kafa Hisbah don ganin an aiwatar da dokar, yana mai cewa hakan zai hana lalata da barna
  • A cewar gwamnatin jihar, wannan mataki na hana giya ya samo asali ne daga karuwar aikata laifuka da barna a Maiduguri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno -Babban Limamin filin jirgin sama na kasa da kasa da ke Maiduguri ya yi magana bayan haramta sayar da giya a Borno.

Sheikh Muhammad Ibrahim Adam, ya yaba wa Gwamnan Borno, Babagana Zulum, bisa daukar wannan mataki da ya yi.

An yabawa Zulum kan haramta giya a Borno
Malamin Musulunci ya kwarara yabo ga Zulum a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar watsa labarai da tsaro ta cikin gida ta jihar ta fitar a ranar Lahadi 11 ga watan Mayun 2025, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Zulum na haramta giya a Borno

Hausa Legit ta ruwaito cewa Zulum ya sanar da dokar ne ranar Talata 6 ga watan Mayun 2025 a wajen kaddamar da kwamitin rusau da yaki da munanan dabi’u.

Gwamnan ya bayyana cewa hana sayar da giya ya samo asali ne daga yawaitar rikice-rikice, kungiyoyin asiri, karuwanci da shaye-shaye.

Musabbabin haramta siyar da barasa a Borno Zulum ya zargi jami’an tsaro da zuga fararen hula aikata laifuffuka, karuwanci da sauran miyagun dabi’u da ke haddasa matsalar tsaro.

Ya ba kwamitin karfin guiwa don yakar miyagun mutane a Maiduguri da kewaye, da kuma dakile lalacewar tarbiyya a cikin al’umma.

Gwamnan ya ce haramta barasa na da nasaba da yawaitar kungiyoyin asiri, fada tsakanin bata gari, da kisan gilla a Borno.

Zulum ya hada da sojoji, ’yan sanda, NSCDC da 'Civilian JTF' a cikin kwamitin domin tabbatar da cikakken yaki da laifuka.

Malamin Musulunci ya yabawa Zulum a Borno
Malamin Musulunci ya yabi Zulum kan haramta sayar da giya a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Twitter

Haramta giya: Malamin Musulunci ya yabi Zulum

Babban limamin ya ce tabbas wannan matakin ya zo daidai lokacin da aka fi buƙatarsa duba da yananin tarbiya a jihar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa limamin ya kammala da addu’o’i na zaman lafiya, hadin kai da cigaba ga jihar Borno da kasa baki daya.

A cewarsa:

“Limamin ya bukaci gwamnati ta kafa hukumar Hisbah a jihar domin kare dabi’u da dokokin addini tare da yaki da munanan dabi’u.
“Sha da maye ko wani abu mai sa buguwa haramun ne ga dukkan addinai, domin suna bude kofa ga barna da laifuka."

Zulum ya haramta sayar da fetur a Bama

A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum ya bada umarnin gaggauta haramta sayar da fetur a fadin karamar hukumar Bama.

Umarnin ya shafi har da yankin Banki a cikin bayanan da gwamnati ta fitar da suke cewa matakin na da nasaba da kokarin gwamnatin jihar Borno na dakile ta’addanci.

Farfesa Zulum ya yi gargadi da cewa za a hukunta duk wanda aka kama da karya wannan doka ba tare da nuna bambanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.