
Jihar Zamfara







Bayan sanar da sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar, gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana fita daga wayewar gari zuwa dare a jihar don hana tashin hankali.

Dauda Lawal Dare na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara. Akwai wasu muhimman abubuwan sani dangane da rayuwar sa.

Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Zamfara ke fitowa a zaben bana na ba da mamaki. An ce dan takarar PDP ne kan gaba a zaben na bana da aka yi a jihar Arewa.

Shugaban kamfen Bola Tinubu a Arewa maso Yamma watau Gwamna Matawalle Ya fadi zabe. Lawal Dare ya samu kuri’u 377,726, Bello Mohammed Matawalle yana da 311, 976

Yanzu muke samun labarin yadda wasu tsageru suka yi awon gaba da wasu manyan jami'an hukumar zabe ta INEC da ke dauke da sakamakon zaben da aka yi a Maradun.

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara kuma ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jihar a inuwar jam'iyyar APC, ya rasa kujerar sa a hannun ɗan jam'iyyar PDP.
Jihar Zamfara
Samu kari