Yadda Elon Musk Ya Zama na Farko da Ya Mallaki Dala Tiriliyan 1 a Duniya

Yadda Elon Musk Ya Zama na Farko da Ya Mallaki Dala Tiriliyan 1 a Duniya

  • Elon Musk ya zama mutum na farko a duniya da dukiyarsa ta haura tiriliyan 1 na dala bayan farashin IPO na SpaceX ya ɗaga ƙimar dukiyarsa
  • An saka farashin hannun jarin SpaceX a kan dala 135, wanda ya sa kason Musk na kashi 42 cikin 100 a kamfanin ya kai kimanin dala biliyan 648
  • Ana sa ran IPO ɗin zai samar da dubban sababbin attajirai masu miliyoyin daloli daga cikin ma’aikatan SpaceX da masu zuba jari a fadin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Elon Musk ya zama mutum na farko a tarihin duniya da dukiyarsa ta zarce dala tiriliyan 1 bayan fara sayar da hannayen jarin SpaceX ga jama’a (IPO), wanda ya ɗaga ƙimar kadarorinsa zuwa matakin.

SpaceX ta saka farashin hannun jarinta a kan dala 135 kafin fara cinikinsa a kasuwa, lamarin da ya haɓaka dukiyar Musk zuwa sama da dala tiriliyan 1.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Elon Musk a wajen wani taro
Attajirin duniya, Elon Musk yana dariya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dukiyar Elon Musk ta kai dala tiriliyan 1

Kafin IPO ɗin, mujallar Forbes ta kiyasta dukiyar Musk a kusan dala biliyan 813, wanda tuni ya sanya shi mutum mafi arziki a duniya da tazara mai yawa.

Wannan sabon matsayi ya sa Musk ya zarce sauran attajiran duniya nesa ba kusa ba, inda wanda ke matsayi na biyu, Larry Page, wanda ya kafa Google tare da wasu, ke da dukiyar da aka kiyasta a kusan dala biliyan 288.

BBC ta wallafa cewa an fara cinikin hannayen jarin SpaceX a kasuwar Nasdaq da alamar “SPCX” ranar Juma’a bayan bude kasuwa da ƙarfe 9:30 na safe.

Yawan buƙatar masu zuba jari ya nuna ƙarin amincewa da fasahar zamani, kasuwancin intanet ta tauraron dan adam da kuma burin kamfanin a fannin AI.

Dukiyar Musk na iya ƙaruwa idan farashin hannun jarin SpaceX ya karu, amma idan farashinsa ya ragu, hakan na iya mayar da dukiyarsa ƙasa da tiriliyan 1.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

Musk ya fi wasu kasashe kudi

Wannan nasara ta kai dukiyar Elon Musk matakin da ya yi daidai da tattalin arzikin wasu manyan ƙasashe a fadin duniya a yau.

Ƙasashe kaɗan ne kawai a duniya ke da jimillar tattalin arzikinsu (GDP) sama da dala tiriliyan 1 a shekara, lamarin da ya sa wannan nasara ta zama sanadin kafa tarihi a fannin tattalin arzikin duniya.

Musk ya fara samun suna a duniya ta hanyar kamfanin Tesla, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa motocin lantarki, da kuma SpaceX wanda ya kawo sauyi a harkar zirga-zirgar sararin samaniya.

Attajirin duniya, Elon Musk
Elon Musk a gaban motar lantarki da ya ke kerawa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daga bisani ya faɗaɗa kasuwancinsa ta hanyar sayen dandalin X, wanda a baya ake kira Twitter, a kan dala biliyan 44 a shekarar 2022.

Dukiyar Abdulsamad Rabiu ta ƙaru

A wani labarin, kun ji cewa Abdulsamad Rabiu, mutum na biyu mafi arziki a Najeriya, yanzu yana da dukiyar da ta kai dala biliyan 19.7.

Dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 9.53 a wannan shekara, wanda ya rage masa kusan dala miliyan 300 kacal kafin ya kai matakin dala biliyan 20.

Har yanzu Alhaji Aliko Dangote da ya kafa matatar man fetur a Naeriya ne mutum mafi arziki a Afirka da dukiyar da ta kai dala biliyan 36.7.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng