Lokaci Ya Yi: An Shiga Rudani kan Yanayin da Wani Babban Jami'in Kwastam Ya Rasu a Bauchi
- An tsinci gawar wani babban jami’in Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Lumi Elisha Gwamis, wanda ya rasu yana da shekaru 44
- Mutuwar jami'in na NCS ta jefa al’ummar garin Boi da ke karamar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi cikin alhini da jimami
- Hukumar Kwastam ta musanta rade-radin da ke yawo cewa ya kashe kansa ne a wurin da aka tsinci gawarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Al’ummar garin Boi da ke karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi sun shiga jimami bayan rasuwar wani babban jami’in Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Lumi Elisha Gwamis.
Rahotanni sun nuna cewa rasuwar Gwamis ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mazauna yankin, inda ake ta yada bayanai mabambanta kan musabbabin mutuwarsa.

Source: Original
Sai dai rahoton Daily Trust ya nuna cewa har zuwa yanzu babu wata hukuma da ta tabbatar da irin wadannan zarge-zarge, yayin da ake dakon ainihin abin da ya yi ajalinsa.
Gwamis, babban ɗa ga tsohon shugaban ƙaramar hukumar Bogoro, Hon. Elisha Tula Gwamis, ya mutu ne a gidansu sakamakon abin da wasu suka bayyana a matsayin rashin lafiya da damuwa.
Mahaifinsa ya bayyana alhininsa
A yayin wata ziyarar ta’aziyya da aka kai wa iyalansa ranar Litinin, mahaifinsa, Hon. Elisha Tula Gwamis, ya bayyana matukar kaduwarsa da rasuwar dan nasa.
A cewarsa, marigayin yana cikin koshin lafiya kuma babu wata alamar da za ta nuna cewa irin wannan lamari zai faru.
"Ɗana Lumi yana cikin koshin lafiya kuma yana gudanar da harkokinsa yadda ya kamata. Babu wanda ya yi tunanin abin da ya faru zai faru, sai dai muka samu labarin rasuwarsa, wanda ya girgiza mu matuka," in ji shi.
Hukumar Kwastam ta yi karin haske
A halin da ake ciki, Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Zone D da ke Bauchi, ta yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa jami’in ya kashe kansa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Abdullahi, ya ce babu wani sahihin bayani da ke goyon bayan irin wadannan rade-radi, kamar yadda Leadership ta rahoto shi yana fada.

Kara karanta wannan
Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, Sarkin Gazargamu ya riga mu gidan gaskiya a Masar

Source: Facebook
Ya bayyana cewa marigayin ya dawo Bauchi ne bayan an canza masa wurin aiki daga tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island, inda ya je ofishin domin kammala wasu takardu kafin ya tafi hutunsa na shekara.
"Abin da mahaifinsa ya sanar da mu shi ne cewa yana fama da rashin lafiya. Ya zo ofis tare da mahaifinsa domin kammala takardun sauya wurin aikinsa, sannan ya tafi hutun shekara wanda ya cancanta," in ji Abdullahi.
Ya kara da cewa hukumar ta samu labarin rasuwarsa ne daga mahaifinsa, yana mai jaddada cewa ba za su iya tabbatar da wani abu ba face bayanan da iyalansa suka bayar.
Tsohon shugaban UNILORIN ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da rasuwar tsohon shugaban jami'ar tarayya da ke Ilorin a jihar Kwara, (UNILORIN), Farfesa AbdulGaniyu Ambali.
Majiyoyi daga iyalinsa sun bayyana cewa Ambali ya rasu da tsakar dare, ‘yan sa’o’i bayan ya halarci sallar Isha’i a wani masallaci da ke kusa da gidansa.
Mai magana da yawun jami'ar UNILORIN , Kunle Akogun, ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar, inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa.
Asali: Legit.ng
