Mutuwa Ta Girgiza Sarakunan Najeriya, Osi Balogun Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Ibadan

Mutuwa Ta Girgiza Sarakunan Najeriya, Osi Balogun Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Ibadan

  • Osi Balogun na masarautar Ibadanland da ke jihar Oyo, Oba Olubunmi Isioye-Dada, ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya
  • Rahotanni daga wasu majiyoyi sun nuna cewa basaraken ya rasu a gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya
  • Rasuwarsa ta haifar da gurbi a tsarin sarautar Ibadan wanda zai jawo karin girma ga wasu hakimai da sarakuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, Nigeria - Al’ummar jihar Oyo sun shiga alhini bayan rasuwar Osi Balogun na Ibadanland, Oba Olubunmi Isioye-Dada, wanda ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wata majiya daga cikin masu fada a ji a fadar Ibadanlamd da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da rasuwar basaraken a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Osi Balogun of Ibadanland.
Osi Balogun na Ibadanland, Oba Isioye-Dada, lokacin da Gwamna Seyi Makinde ke tabbatar da nadinsa Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Basarake ya rasu a birnin Ibadan

Majiyar ta shaida wa jaridar Tribune Nigeria cewa Oba Isioye-Dada ya rasu ne a gidansa da ke Ibadan bayan ya yi fama da rashin lafiya na dan wani lokaci.

Kara karanta wannan

"Talauci da jahilci sun yi kamari a Arewa": Sarki Sanusi II ya ba da mafita

Majiyar ta kara da cewa jim kadan bayan samun labarin rasuwar, tawagar Omo Oye ta tafi gidan marigayin domin gudanar da al’amuran da suka dace da kuma nuna alhini ga iyalansa da masoyansa.

Wane ne Oba Isioye-Dada?

Kafin rasuwarsa, Oba Olubunmi Isioye-Dada ya kasance Osi Balogun na Ibadanland, daya daga cikin manyan mukaman gargajiya a tsarin sarautar Ibadan.

An san shi da taka muhimmiyar rawa wajen kula da al’amuran gargajiya da ci gaban masarautar Ibadan, tare da ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’umma.

Rasuwar za ta sauya tsarin mukamai

Rasuwar Osi Balogun ta bude gurbi a jerin mukaman masarautar Ibadan, lamarin da zai haifar da karin girma ga wasu hakimai da sarakuna a bangaren Balogun.

Bisa tsarin sarautar Ibadan, idan wani babban hakimi ya rasu ko ya bar mukami, wadanda ke kasa da shi sukan samu karin matsayi domin cike guraben da aka samu.

Bayan amincewar Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, Sanata Sharafadeen Ali, wanda ke rike da mukamin Ekaarun Balogun, zai samu karin girma zuwa Ekerin Balogun na Ibadanland.

Haka kuma, Oba Akeem Mobolaji Adewoyin zai tashi daga mukamin Ekerin Balogun zuwa Asipa Balogun na Ibadanland, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Ba mu muka kar zomon ba': Hausawa sun yi zanga zanga bayan sace daliban Oyo

Masu bibiyar harkokin sarauta a Ibadan sun bayyana cewa wadannan sauye-sauye na daga cikin tsarin gargajiya da ake bi wajen tabbatar da dorewar shugabanci a masarautar.

Jihar Oyo.
Taswirar jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana jiran sanarwar masarauta

A halin yanzu, jama'a da masoya marigayin na ci gaba da aika sakonnin ta'aziyya ga iyalansa da masarautar Ibadanland.

Ana sa ran fadar Olubadan za ta fitar da cikakken bayani kan jana'izar marigayin da kuma matakan da za a dauka game da sauye-sauyen mukaman sarautar da rasuwarsa ta haifar.

Sarkin Gazargamu ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Gazargamu na jihar Yobe, Mai Martaba Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, ya rasu bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa sarkin ya rasu ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026 a birnin Alkahira na ƙasar Masar.

An bayyana marigayin a matsayin uba, jagora kuma sarki wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa da bil’adama hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262