Kotu Ta Yi Umarni a Kama Tsohon Ministan Tinubu da Ya Samu Takarar Gwamna

Kotu Ta Yi Umarni a Kama Tsohon Ministan Tinubu da Ya Samu Takarar Gwamna

  • Rahotanni sun nuna cewa Babbar Kotun Tarayya ta umarci ICPC ta kama tsohon minista, Uche Nnaji kan zargin amfani da takardun bogi
  • ICPC ta ce ya ki amsa gayyatar bincike kan zargin wanda hakan ya kai ga kotu ta ba da izinin ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo
  • Bayan murabus a gwamnatin Bola Tinubu, tsohon ministan ya koma jam'iyyar PDP kuma ya samu titikin jam'iyyar na takarar gwamna a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar ICPC da ta kama tsohon kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, bisa zargin yin amfani da takardun bogi.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan wani bukatar gaggawa da ICPC ta gabatar a karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1160/2026.

Kara karanta wannan

An tafka asara mai yawa da gobara ta babbake shaguna a wata kasuwa a jihar Kano

Tsohon ministan, Uche Nnaji
Uche Nnaji kafin ya sauka daga minista. Hoto: Uche Nnaji
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa hakan ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ta wallafa a watan Oktoba na shekarar 2025.

Bukatar gaggawa da aka shigar

An shigar da takardar bukatar gaggawar ta ICPC mai dauke da ranar 3 ga Yunin 2026 ne a ranar 4 ga Yuni, kamar yadda wata takardar kotu ta nuna.

Hukumar ta hannun David Nelson ta yi rantsuwa domin goyon bayan bukatar, sannan ta kuma mika rubutacciyar hujja a kotun.

An sanya Nnaji a matsayin wanda ake kara shi kadai, yayin da gwamnatin tarayya ta hannun ICPC ita ce mai shigar da kara.

Abubuwan da ICPC ta nema

Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya shaida wa kotun cewa bukatar ta samo asali ne daga gazawar Nnaji wajen amsa gayyatar da hukumar ta aika masa domin gudanar da bincike kan zargin da ake masa.

ICPC ta roki kotun da ta ba ta izinin ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ta hanyar jaridun kasa, kafafen sada zumunta ko wasu hanyoyin yada labarai saboda kin amsa gayyatar bincike.

Kara karanta wannan

Bam ya tarwatse da bayin Allah a Zamfara, mutane da dama sun rasa rai

Hukumar ta kuma nemi kotun da ta bayar da sammacin kama shi, tare da umartar jami’anta ko wasu jami’an tsaro har ma da fararen hula su gano inda yake, su kama shi sannan su mika shi ga ICPC domin gudanar da bincike.

Uche Nnaji a birnin tarayya Abuja
Uche Nnaji yayin hira da manema labarai. Hoto: Uche Nnaji
Source: Facebook

Kotu ta ce a kama Nnaji

A hukuncinta, kotun ta amince da bukatar ICPC na ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ta kowace hanyar yada labarai.

Kotun ta kuma bayar da sammacin kama shi tare da umartar jami’an ICPC ko wasu jami’an tsaro, har da fararen hula, su gano shi su kama shi sannan su mika shi ga hukumar domin ci gaba da bincike.

A watan Mayun 2026 Nnaji ya koma jam'iyyar PDP tare da neman tikitin takarar Gwamnan jihar Enugu domin fafatawa a zaben 2027.

Maganar neman kama Mele Kyari

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin majalisar dattawa ya bayar da umarnin kama tsohon shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari.

Kwamitin ya bukaci a kama shi saboda ci gaba da kin amsa gayyatar da aka yi masa dangane da binciken da ake yi kan kudin kamfanin.

Sai dai daga baya bayan zama da Majalisar dattawa ta yi ta nesanta kanta daga matakin da kwamitin ya dauka game da Mele Kyari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng