Rigima Ta Kunno Kai a NDC da Shugaban Kwamitin Zabe Ya Mika Sunayen 'Yan Takara ga INEC

Rigima Ta Kunno Kai a NDC da Shugaban Kwamitin Zabe Ya Mika Sunayen 'Yan Takara ga INEC

  • Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar NDC yayin da shugaban kwamitin zaben fidda gwani ya aika sunayen 'yan takara kai tsaye zuwa INEC
  • Wasu jiga-jigan jam'iyyar NDC reshen jihar Abia sun ce aikin mika sunayen 'yan takara hakkin uwar jam'iyya ta kasa ne
  • Matakin na iya haifar da rikici da ka iya kai wa gaban kotu idan jerin sunayen ya bambanta da wanda shugabancin NDC na kasa zai mika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Rigima ta kunno kai a jam'iyyar NDC bayan da aka bayyana cewa shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jihar Abia, Cif Asukewe Ikoawaji, ya ya mika sunayen 'yan takara ga hukumar INEC.

Bayanai sun nuna cewa ya aika jerin sunayen 'dan takarar gwamna, yan takarar majalisun tarayya da na jiha na NDC daga jihar Abia kai tsaye zuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Kara karanta wannan

Mutane sun huta, jami'an tsaro sun yi ajalin hatsabibin dan bindiga, Baccujo

Tutar NDC.
Tambarin jam'iyyar adawa ta NDC a Najeriya Hoto: NDC
Source: Facebook

Rikici ya sake kunno kai a NDC

Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam'iyyar, inda wasu mambobi ke ganin cewa an karya ka'idojin da suka shafi mika sunayen 'yan takara ga hukumar zabe.

Wasu jiga-jigan NDC da suka san yadda tsarin ke gudana sun bayyana cewa ikon sanarwa da mika sunayen wadanda suka yi nasara a zabukan fidda gwani na hannun shugabancin jam'iyya na kasa.

A cewarsu, shugaban jam'iyyar na kasa da sakatarensa ne ke da hurumin aikawa da sunayen 'yan takara zuwa INEC bayan kammala dukkan matakan da suka dace.

Abin da ke cikin wasikar Ikoawaji

Takardun da manema labarai suka gani sun nuna cewa Ikoawaji ya rubuta wa shugaban INEC wasika ta hannun kwamishinan zabe na jihar Abia a ranar 30 ga Mayun 2026.

A cikin wasikar mai taken "Sakamakon Zaben Fidda Gwani na NDC a Jihar Abia", ya bayyana cewa an kammala tattara sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 29 ga Mayun 2026 daga kananan hukumomi da mazabu a jihar.

Kara karanta wannan

'Nigeria Air': EFCC ta tona yadda Ministan Buhari ya yaudari 'yan kasa da jirgin aro

Ikoawaji ya kuma sanar da INEC cewa an riga an aika da sakamakon zuwa hedikwatar jam'iyyar ta kasa da ke Abuja bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Ya hada da kwafin sanarwar nadin kwamitin zabe, dokokin gudanar da zaben da kuma sakamakon zaben domin INEC ta dauki matakin da ya dace, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Shugaban INEC.
Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Jiga-jigan NDC sun hango matsala

Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar NDC sun nuna damuwa cewa aika sakamakon zabe kai tsaye zuwa INEC daga shugaban kwamitin zabe na iya haifar da rikice-rikicen doka da na cikin gida.

Sun ce matsalar na iya tsananta idan jerin sunayen da Ikoawaji ya mika ya bambanta da wanda shugabancin jam'iyyar NDC na kasa zai aika daga baya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, shugabancin jam'iyyar NDC na kasa da kuma INEC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

NDC ta yi kura-kurai a zaben fidda gwani

A wani labarin, kun ji cewa jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson ya amince cewa an samu wasu kura-kurai a zaɓukan fitar da gwani a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun tayar da hayaniya a Legas, an yi zanga zanga kan zaben fitar da gwani

Sanata Seriake Dickson ya shaidawa 'yan jam'iyya cewa NDC na ƙoƙarin shawo kan ƙalubalen da ke tattare halin da ake ciki a yanzu.

Ya bayyana tausayinsa ga masu neman takara a cikin jam'iyyar da ba su samu abin da suka nema ba, tare da cewa har yanzu ana tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262