Gwamnan Buni Ya Nada Tsohon Dan Majalisa Sarkin Ngazargamu a Yobe
- Rahoto ya nuna cewa an naɗa Yarima Ibn Mahmud a matsayin sabon Mai Ngazargamu bayan rasuwar Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam
- Gwamna Buni ya buƙaci sarkin ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin
- Mahmud yana da gogewa mai yawa, ya taɓa zama Turakin Ngazargamu da kuma kwamishinan harkokin kiwon dabbobi na jihar Yobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe – Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya naɗa Yarima Ibn Mahmud a matsayin sabon Mai Ngazargamu a ranar Juma'a, 12 ga Yunin 2026.
Naɗin Mahmud ya biyo bayan rasuwar tsohon Mai Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam bayan fama da rashin lafiya da ya yi.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: An shiga rudani kan yanayin da wani babban jami'in Kwastam ya rasu a Bauchi

Source: Twitter
Kamar yadda The Punch ta ruwaito, mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Mohammed Goje, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a.
Kiran Gwamna Buni ga Sarkin Ngazargamu
Gwamna Buni ya buƙaci sabon sarkin da ya yi amfani da dimbin ƙwarewarsa wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.
Ya taya sabon Sarkin da al’ummar Masarautar Ngazargamu murna yana cewa:
“Ina taya sabon Mai Ngazargamu da ɗaukacin al’ummar masarautar murnar wannan naɗi.
"Ina kira ga mai martaba da ya yi amfani da tarin ƙwarewarsa wajen haɗa kan jama’a, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin lumana, tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki a masarautar, jihar Yobe da Najeriya baki ɗaya.”
Matsayin da sarkin ya rike a baya
A cewar sanarwar, Ibn Mahmud ya yi shekaru 16 yana matsayin Turakin Ngazargamu, sannan ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin Jihar Yobe.
Sabon Sarkin ya kuma yi aiki a majalisar zartarwa ta jihar Yobe, inda ya kasance kwamishinan harkokin kiwon dabbobi kafin ɗaga shi zuwa karagar mulki.
Kiran Buni ga jama'ar jihar Yobe
Gwamna Mai Mala Buni ya buƙaci al’ummar masarautar da su ba sabon sarkin cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukansa.
Ya ce:
“Ina kira ga al’ummar masarautar da su ba sabon sarkin dukkan goyon bayan da yake buƙata domin ya gudanar da ayyukan ofishinsa cikin ƙwazo, inganci da nasara, domin amfanin jama’a da ci gaba da wanzuwar zaman lafiya, haɗin kai da wadata a masarautar.”

Kara karanta wannan
Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, Sarkin Gazargamu ya riga mu gidan gaskiya a Masar
Shettima ya kai ziyarar ta’aziyya
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci wata babbar tawaga domin halartar sallar jana’izar marigayi Mai Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam, tare da miƙa ta’aziyyarsa.
Sanata Shettima ya ce ya je jihar ne domin isar da ta’aziyyar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatin tarayya ga gwamnati da al’ummar jihar kan rasuwar sarkin.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Yobe, Mamman Muhammad ya wallafa a Facebook cewa Shettima ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga gwamnatin da al’ummar jihar Yobe da ma Najeriya baki ɗaya.
Sarki Sanusi II ya ci gyaran Shettima
A wani rahoton, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II, ya ƙalubalanci kalaman da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima kan Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu.
Sanusi ya ce akwai gyara a kalaman Shettima na cewa jihar Legas ce ta samar da manyan 'yan kasuwan da suka fi kowa kudi a Najeriya a yau.
Sarkin ya bayyana cewa Kano ce, ba Legas ba, ta gina tushen kasuwancin attajirin Afirka Aliko Dangote da kuma hamshaƙin ɗan kasuwa Abdul Samad Rabiu.
Asali: Legit.ng

