Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Ma'aikata Sun Karɓi Albashin da Ba Su Taɓa Gani ba a Zamfara

Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Ma'aikata Sun Karɓi Albashin da Ba Su Taɓa Gani ba a Zamfara

  • Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya cika alƙawarin da ya ɗauka na fara biyan mafi karancin albashi N30,000 ga ma'aikatan jihar
  • Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya ce tuni aka biya albashin watan Yuni saboda zuwa Babbar Sallah
  • Ya ce gwamnati mai ci za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin kara inganta walwala da jin daɗin ma'aikatan gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka yayin ganawa da shugabannin ƴan kwadago a makonnin da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Gwamna Dauda Lawal.
Zamfara ta fara biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata N30,000 da albashin Yuni Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamna Lawal dai ya sha alwashin fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma'aikatan jihar Zamfara domin ƙara masu kwarin guiwa, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An biya albashin Yuni a Zamfara

A wata sanarwa ranar Jumu'a, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya tabbatar da cewa Dauda Lawal ya cika alƙawarin da ya ɗauka, Premium Times ta kawo.

Ya ce ma'aikatan gwamnatin Zamfara sun fara ganin alat ɗin albashin watan Yuni tun daga ranar 12 ga wata gabannin fara bukukuwan Babbar Sallah.

Ya ce kafin yanzu ma’aikatan gwamnati suna karɓan albashin N7,000 ne duk wata, inda ya ce gwamnati mai ci ta kudiri aniyar ganin ta inganta walwalar ma’aikata.

Dauda Lawal ya kafa tarihi

“Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta biya albashin watan Yuni domin tallafa wa ma’aikata wajen shirin Babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Bayan Dikko Radda ya buɗe kofa, Gwamna a Arewa ya ba ma'aikata N10,000 goron sallah

“Hakan kuma ya zo daidai da cika alkawarin da gwamna ya ɗauka a watan jiya na aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na N30,000. Kafin yanzu N7000 ne albashi mafi ƙanƙanta.
"Gwamnati za ta ci gaba da kokarin kawo gyara da sake farfado da walwala da jin daɗin ma'aikatan jihar Zamfara."

- Sulaiman Bala Idris.

Umar Tsafe, wani ma'aikacin gwamna a Zamfara ya tabbatar da ƙarin albashin da gwamna ya yi masu a watan Yuni.

"Wannan gaskiya ne mun samu karin albashi, muna yiwa gwamna fatan alheri da addu'ar Allah ya ci gaba da yi masa jagora," in ji shi.

Gwamnatin Tinubu ta bada hutun kwanaki 2

A wani rahoton kuma Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin da Talata, 16 da 17 ga watan Yuni a matsayin hutun babbar Sallah ta bana 2024.

Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan ranar Jumu'a, ya kuma taya ɗaukacin al'ummar Musulmi murna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262