Wulakanta Naira: Kotu Ta Yanke wa Fitattun 'Yan TikTok 2 Hukuncin Ɗaurin Wata 6

Wulakanta Naira: Kotu Ta Yanke wa Fitattun 'Yan TikTok 2 Hukuncin Ɗaurin Wata 6

  • An yanke wa wasu fitattun 'yan TikTok biyu, TobiNation da TDollar, hukuncin ɗaurin watanni shida saboda wulakanta Naira a Legas
  • Hukuncin ya biyo bayan kame su tare da gurfanar da su da hukumar EFCC ta yi bisa zargin keta dokar Babban Bankin Najeriya (CBN)
  • Kotun ta amince da bidiyo da bayanan da EFCC ta gabatar da su a matsayin shaida, kuma ta yanke musu hukuncin ɗauri ko kuma biyan tara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi ta yanke wa wasu 'yan TikTok, TobiNation da TDollar, hukuncin ɗaurin watanni shida a kan wulakanta Naira.

An ce hukuncin kotun ya biyo bayan kama su da gurfanar da su da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi.

Babbar kotun tarayya a Legas ta yanke wa fitattun 'yan TikTok, TDollar, TobiNation hukuncin daurin wata 6
Fitattun 'yan TikTok, TDollar da TobiNation. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Kotu ta daure 'yan TikTok na wata 6

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, EFCC ta ce an yanke wa fitattun masu wasan barkwaci a TikTok ɗin hukuncin ɗaurin wata shida kowanne a ranar 8 ga Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alexander Owoeye, wanda ya jagoranci shari'ar, ya yanke hukuncin ne bayan da dukkan waɗanda ake zargi suka amsa laifinsu a kan tuhumar wulakanta Naira.

An tuhumi TDollar, wanda asalin sunansa Babatunde Peter Olaitan, da TobiNation, wanda ainihin sunansa Tobilola Olamide, da laifin keta dokar CBN ta hanyar watsa takardun Naira a wajen biki.

EFCC ta kama tare da gurfanar da 'yan TikTok

Lauyan masu gabatar da ƙara, C.C. Okezie da H.U. KofarNaisa, sun gabatar da shaidu ta hannun Ibrahim Bukar, wani jami'in bincike na EFCC.

Bukar ya shaida wa kotun cewa hukumar ta fara "bincike mai zurfi a kan jaruman TikTok ɗin" a ranar 10 ga Afrilu, 2025, bayan bullar wani bidiyo da ya nuna TDollar yana watsa Naira a taro.

Jami'in bincike na EFCC ya shaida wa kotun cewa:

"Bayan amincewar daraktan shiyya, an aika wa wanda ake tuhuma wasiƙar bincike, inda aka nemi ya ba da bayani game da bidiyon.
"Wanda ake tuhumar ya kai rahoto ga sashen ayyuka na musamman (SOT) a ranar 5 ga Mayu, 2025, kuma an rubuta bayanansa a ƙarƙashin tsarin gargadi."
Hukumar EFCC ta gurfanar da fitattun 'yan TikTok a gaban babbar kotun tarayya ta Legas
Hedikwatar hukumar EFCC, Abuja. Hoto: @officialEFCC
Asali: Facebook

Kotu ta yi hukunci kan wulakanta Naira

Ya kara da cewa:

"Ya bayyana cewa ya je wani gidan rawa a ranar 8 ga Afrilu, 2025, kuma ya hadu da wasu masoyansa suna lika kuɗi. Ya kuma ce wani masoyinsa ne ya ba shi damin N200, wanda ya yi liki da su a ranar.

Kotun ta karɓi bidiyon da bayanan da aka samu a wajen kotu a matsayin hujja. Masu gabatar da ƙara sun roƙi kotun da ta yanke wa waɗanda ake tuhumar hukunci bisa hujjojin.

Mai shari'a Owoeye ya yanke wa kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar hukuncin ɗaurin watanni shida tare da zaɓin biyan tarar N200,000.

Karanta sanarwar EFCC a nan kasa:

Yaushe mutane za su dauki darasi?

A zantawarmu da Musal Lawal, wani dan kasuwa mazaunin Legas, ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan Najeriya su shiga taitayinsu kan dokokin EFCC.

A cewar Musa Musa Lawal:

"Mutane suna ganin kamar burge wa ne su rika watsa kudi a wajen bukukuwa kuma suna daukar bidiyo suna watsawa a intanet, duk da sun san cewa hakan haramun ne.
"Ko ba don gudun kamu da dauri ba, ya kamata mutane su daina wulakanta Naira, saboda wulakanta Naira tamkar aika sako ne ga 'yan waje cewa ba mu girmama kasar mu."

Musa Lawal ya ce ya kamata a ci gaba da wayar da kan jama'a kan illar wulakanta Naira ta hanyar shirye-shiryen rediyo, talabijin da sauran kafofin sada zumunta.

EFCC ta cafke Murja Kunya kan wulakanta Naira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC ta sake kama fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, a Kano bisa zargin wulakanta Naira a wajen wani taro.

An ruwaito cewa Murja Kunya ta tsere daga belin da aka ba ta a baya, amma jami'an hukumar sun sake cafke ta, lamarin da ya haifar da cece-kuce.

Wannan kamen ya jawo martani daga jama'a, inda wasu ke ganin hakan zai zama darasi ga manyan 'yan soshiyal midiya kan aikata abin da zai jawo masu fushin hukuma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.