Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Watanni 6 Kan Shahararren Dan Daudu, Bobrisky

Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Watanni 6 Kan Shahararren Dan Daudu, Bobrisky

  • A ƙarshe, babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta ɗaure fitaccen ɗan daudun nan, Bobrisky a gidan gyaran hali
  • Mai shari'a Abimbola Awogboro ya yanke wa ɗan daudun hukuncin ɗaurin watanni shida ba tare da zaɓin tara ba ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu
  • Tun a makon jiya ne hukumar yaƙi da marasa gaskiya EFCC ta gurfanar da Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky kan tuhume-tuhume 6

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Babbar kotun tarayya da ke zama a jihar Legas ta yanke wa fitaccen ɗan daudun nan, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky hukunci ranar Jumu'a.

Kotun ta yanke wa shahararren ɗan daudun hukuncin ɗauri a gidan gyaran hali na tsawon watanni shida ba tare da zaɓin tara ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun dira sansanin manyan ƴan bindiga 3 a Arewa, sun kashe da yawa ranar Sallah

Idris Okuneye.
Kotu ta daure Bobrisky na tsawon watanni 6 Hoto: EFCC
Asali: Instagram

Mai shari'a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya ne ya yanke wa ɗan daudun wannan hukunci ranar 12 ga watan Afrilu, 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a makon jiya dai ake tsare da Bobrisky gabanin yanke masa hukunci bayan ya amsa wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ce ta gurfanar da fitaccen ɗan daudun kan tuhume-tuhume guda shida.

Wasu laifuffuka ake tuhumar Bobrisky?

Daga bisani an cire biyu daga cikin tuhume-tuhumen yayin da ya amsa laifin wulaƙanta Naira kuma ya roƙi a masa afuwa kasancewar wannan ne karo na farko.

A yayin da yake yanke hukuncin, mai shari’a Awogboro ya ce hukuncin zai zama izina da gargaɗi ga masu sha’awar cin zarafi da lalata kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Emefiele: Kotu ta ɗauki mataki 1 kan tsohon gwamnan CBN bayan EFCC ta ƙara gurfanar da shi

Alkalin ya kuma yanke hukuncin cewa zaman gidan yarin ya fara ne daga ranar 24 ga Maris, 2024, ranar da aka kama shi, The Nation ta ruwaito.

A ranar 5 ga Afrilu, kotu ta amince da alifin Bobrisky bayan ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa guda hudu na cin zarafin Naira.

Kotu ta bada belin Emefiele

A wani rahoton kuma wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele a kan N50m.

Mai shari’a Rahman Oshodi ya ce Emefiele na da bukatar mutane biyu da za su tsaya masa kuma dole su kasance masu biyan haraji ga Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel