Zaben Fitar da Gwani: Diyar Tinubu Ta Yi Barazanar Jagorantar Zanga Zanga
- ‘Yar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- Mrs Folashade Tinubu-Ojo ta zargi cewa an samu kura-kurai a sakamakon zaben fitar da gwani na mazabu da dama a Lagos
- Ta bukaci shugabannin APC na jiha da na kasa su binciki zaben kafin amincewa da sakamakon, tana gargadin cewa rikici na iya tashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Ƴar Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Mrs Folashade Tinubu-Ojo, ta soki yadda aka yi zaben fitar gwani a APC.
Folashade ta bayyana barazanar yin zanga-zanga kan sakamakon zaben fidda gwani na APC mai mulki a jihar Lagos.

Source: Facebook
Folashade ta ce an karkatar da sakamakon da aka fitar a mazabun Mushin, Agege da Ojokoro domin nuna fifiko ga wasu bangarorin jam’iyya a jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Amaechi ya yi watsi da 'shiryayyen' zaben fitar da gwanin ADC da Atiku ke kan gaba
Gargadin diyar Tinubu kan zaben fitar da gwani
Ta bukaci shugabannin APC su gudanar da bincike cikin gaggawa kafin amincewa da sakamakon, tana gargadin cewa rashin daukar mataki zai iya kawo rikici.
Diyar shugaban kasar ta ce akwai bukatar tabbatar da adalci domin gujewa rugujewar hadin kan jam’iyyar APC kafin babban zaben 2027.
Ta kuma zargi cewa rikici tsakanin kungiyoyin 'Justice Forum' da 'Mandate Group' na kara raba kan jam’iyyar a Lagos.
Folashade ta ce wasu ‘yan jam’iyya suna barin kungiyoyinsu suna shiga wani bangare saboda siyasa ta cikin gida da burin mulki a nan gaba.
Ta bukaci a daina amfani da rarrabuwar kai domin jam’iyya daya ce APC, kowa ya kamata a yi aiki da shi a cikin tsarin siyasa.

Source: Twitter
Lagos: 'Yar Tinubu ta marawa zabin APC baya
Dan siyasar ta kuma jaddada cewa yan kasuwa a Lagos za su ci gaba da goyon bayan Obafemi Hamzat da sauran ‘yan takarar APC a zaben 2027, cewar Daily Post.
A cewarta:
“Mun shirya yin zanga-zanga saboda Seye Oladejo na Mazabar Tarayya ta Mushin 02, Mutiu Olaide Oladeebo na Mazabar Agege 2, da Olotu Ojo na Mazabar Ojokoro, domin mun san sun ci wannan zabe. Kada a bai wa wani daban, umarnin da suka samu kenan.”
Zaben fitar da gwani na APC da aka gudanar a Najeriya ya bar baya da kura yayin da dama ke ganin an yi masu rashin adalci yayin fitar da yan takara game da zaben 2027.
Yan jam'iyyar da dama sun fice daga cikinta a sassan Najeriya ciki har da tsohon mataimakin shugaban majalisa, Ovie Omo-Agege.
An samu yan takarar gwamna 2 a APC
A wani labarin, an ji cewa rikici ya barke a APC reshen Abia bayan fitowar ‘yan takara biyu daga zaben fitar da gwani na gwamna gabanin na shekarar 2027.
Mambobin kwamitin gudanarwar APC 13 sun amince da Henry Ikoh a matsayin dan takarar bai daya bayan janyewar Mascot Uzor Kalu.
Duk da matsayar SWC, an bayyana Eric Opah a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani bayan samun kuri’u 126,977 lamarin da ya jawo matsala a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng
