Zaben Fitar da Gwani: Yawan Kuri’un da Atiku Ya Samu a Jihohin Arewa

Zaben Fitar da Gwani: Yawan Kuri’un da Atiku Ya Samu a Jihohin Arewa

  • An sanar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya yi nasara a zaben fitar da gwani
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Atiku ya samu jimillar kuri’u 1,846,370 a zaben fitar da gwani na jam’iyyar ADC
  • Ya yi fice a Arewa maso Gabas da maso Yamma, inda jihohin Adamawa, Kano, Gombe da Bauchi suka ba shi kuri’u masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya samu jimillar kuri’u 1,846,370 a zaben fitar da gwani a Najeriya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Atiku ya samu nasara a zaben fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a fadin Najeriya baki ɗaya.

Atiku ya yi nasara a zaben fitar da gwanin ADC
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yana jawabi a taro. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Jihar da Atiku ya fi samun kuri'u

Ya fi samun ƙarfi a shiyyoyin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, musamman jihohin Adamawa, Kano, Gombe da Bauchi, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Atiku vs Amaechi: ADC ta sanar da sakamakon zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa a Kano

A jihar Adamawa inda Atiku Abubakar ya fito, ya fi samun kuri'u fiye da sauran jihohin Arewa da ma na kasa baki daya a zaben da aka gudanar.

Majiyoyi daga Punch suka ce Atiku ya samu kuri'u 177,141 yayin ya tashi da kuri'u 155,595 a Kano da ke Arewa maso Yamma.

A yankinsa na Arewa maso Gabas kuma, Gombe ta ba shi kuri'u 136,933 sai kuma Bauchi ya samu kuri'u 115,410, abin da ya nuna ƙarfin siyasar sa a yankin.

Ya kuma samu goyon baya a Kaduna da kuri'u 108,784, Borno 86,084, da Niger 79,206, wanda ya ƙara masa ƙarfi a Arewa.

A Arewa maso Yamma kuma ya yi nasara a Katsina da kuri'u 74,444, Kebbi 65,153, Sokoto 63,823, da Zamfara 60,500.

Masu neman takara sun soki zaben fitar da gwanin ADC
Tsohon gwamna, Rotimi Amaechi, Mohammed Hayatu-Deen da Atiku Abubakar. Hoto: @Mohayatudeen, @atiku, @ChibuikeAmaechi.
Source: Twitter

Kuri'un Atiku a Kudancin Najeriya

A Kudu maso Gabas, ya samu kuri'i 58, 566 a Anambra, Imo 52,222, yayin da Ebonyi suka ba shi 1,210 da Abia 25,153 da suka ba shi mafi karancin kuri’u.

A Kudu maso Kudu, Akwa Ibom ya samu kuri'u 17,623, Cross River 17,461, Rivers kuma 912, mafi ƙaranci a yankin.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

A Kudu maso Yamma kuma Lagos ta ba shi 37,783, Ogun 25,634, Oyo 23,011, wanda ya kammala jimillar kuri’u 1,846,370.

Jihohin Arewa

Kuri'un Atiku

Adamawa

177,141

Bauchi

115,410

Benue

45,760

Borno

86,084

Gombe

136,933

Jigawa

51,238

Kaduna

108,784

Kano

155,595

Katsina

74,444

Kebbi

65,153

Kogi

48,351

Kwara

6,805

Nasarawa

41,649

Niger

79,206

Plateau

47,558

Sokoto

63,823

Taraba

48,523

Yobe

44,841

Zamfara

60,500

Zaben fitar da gwani: Amaechi ya ki amincewa

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya nuna damuwa da sakamakon zaben fitar da gwani na jam’iyyar ADC da ake yi.

Ya ce sakamakon da ake sanarwa “an kirkire shi”, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta bambanta da APC ba idan aka tafka magudi.

Mohammed Hayatu-Deen ma ya ki halartar sanar da sakamakon zaben, yana zargin an yi magudi da rubuta sakamakon karya a wasu yankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.