Yaɗa Bidiyon Batsa: Kotu Ta Ɗaure Wasu 'Yan TikTok 2 a Kano
- Jihar Kano ta dauki matakan tsabtace abubuwan da ake yadawa a intanet, inda wata kotu ta yanke wa 'yan TikTok biyu hukuncin zaman yari
- Rahoto ya nuna cewa an kama Ahmad Isa da Maryam Musa da laifuffukan samu laifin yada bidiyon batsa, wanda ya sabawa dokokin jihar Kano
- Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ce ta kama su bayan korafe-korafen jama’a game da bidiyon da suke yadawa
- Kotun Majistare ta Kano ta yanke musu hukunci bayan sun amsa laifinsu, tare da ba su damar biyan tarar N100,000 domin gujewa zaman gidan yari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Ana ci gaba da daukar matakan da suka dace na tsabtace abubuwan da ake yadawa a intanet da kuma daidaita tarbiyar mazauna jihar Kano.
A wannan karo, rahoto ya nuna cewa wata kotu a jihar ta yankewa wasu 'yan TikTok hukuncin zaman gidan wakafi na shekara guda kowannensu.

Asali: Getty Images
Hukumar tace fina finai ta cafke 'yan TikTok 2
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an samu 'yan TikTok din biyu da laifin yada bidiyon batsa, wanda ya saba da da'awar gyaran tarbiya ta jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka yankewa hukuncin, Ahmad Isa da Maryam Musa dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro.
Tun da fari, an ce hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ce ta cika hannunta da 'yan TikTok din.
An ce hukumar tace fina finan ta samu korafe-korafe a kan bidiyon batsa da wadanda aka yankewa hukuncin suke yadawa a shafukansu na TikTok.
Rahoton ya ce hukumar ta gurfanar da 'yan Tiktok din a kan tuhume-tuhumen da suka shafi hada baki don aika laifi da yada bidiyon batsa.
Kotun Kano ta yankewa 'yan TikTok hukunci

Asali: Original
Kotun Majistare da ke Norman’s Land a karamar hukumar Fagge, jihar Kano ta yankewa Ahmad da Maryam hukunci bayan sun amsa laifinsu.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
Kafin su amsa laifin, sai da, Barista Garzali Bichi, lauyan gwamnatin jihar Kano, ya karanta wa wadanda ake kara tuhume-tuhumen da ake yi masu da suka hada baki tare da yada bidiyon banza a dandalin sada zumunta.
Daga nan ne alƙaliyar kotun, Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan ta yanke masu hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.
Sai dai Mai Shari’a Hadiza ta ba wadanda ake tuhumar zaɓin biyan tarar N100,000 kowanne, tare da yi masu nasiha a kan zama mutanen kwarai a cikin al'umma.
Saurayi ya siyawa 'yar TikTok gidan N55m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani saurayi ya gaji da zaman fitacciyar 'yar TikTok, Maryam Sa’idu a otel, ya siya mata gida mai darajar Naira miliyan 55.
Maryam Sa’idu ta bayyana cewa daga yanzu ta daina kwana a dakunan otel, domin za ta koma sabon gidanta da aka cika shi da kayan Naira miliyan 22.

Kara karanta wannan
'An yi zalunci': Shekarau ya fadi alakarsa da Kwankwaso bayan tono abin da ya faru tsakaninsu
Sai dai wannan ci gaban ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu ke ganin matashiyar ta yi nisan da ba za ta ji kira ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng