Sojoji Sun Cafke Tsohuwa Mai Taimakon 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

Sojoji Sun Cafke Tsohuwa Mai Taimakon 'Yan Ta'addan Boko Haram a Borno

  • Dubun wata mata mai taimakon 'yan ta'addan ISWAP/Boko Haram ta cika bayan ta fada komar dakarun sojojin Najeriya
  • Dakarun sojojin sun cafke matar ne dauke da kayayyaki wadanda ta yi niyyar kai wa ga danta wanda yake dan ta'adda ne a cikin daji
  • Hukumomi sun bayyana cewa an tsare matar wadda ta kwana biyu a duniya don gudanar da bincike cikin tsanaki domin sanin mataki na gaba da za a dauka a kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na Bataliya ta 196 da ke gudanar da ayyuka a karkashin rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai, sun kama wata mata da ake zargi da zama mai taya ƙungiyar Boko Haram/ISWAP aiki.

Dakarun sojojin sun kama matar ne lokacin da suke gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke yaro 'dan shekara 15 da zargin ayyukan ta'addanci

Sojoji sun cafke mai taimakon Boko Haram a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayun 2026.

An cafke mai taimakon 'yan ta'adda a Borno

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wadda ake zargin, an bayyana sunanta da Mrs Kellu Alhaji Abba, ’yar shekara 50.

Dakarun sojojin sun kama ta ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe ranar Laraba, 20 ga watan Mayun 2026 a wurin bincike na rukunin 'C Company 7 Platoon'.

Majiyoyin sun ce wadda ake zargin, mace ’yar ƙabilari Kanuri da ke zaune a yankin Lawanti a garin Baga, an tare ta ne yayin da ake zarginta da kai wa ɗanta kayan abinci da sauran kayan buƙatu.

An dan nata da Modu Mustapha, wanda ake zargi ɗan ta'adda ne da ke gudanar da ayyukansa a yankin Dumba.

Sojoji sun kwato kayayyaki a hannunta

A cewar majiyoyin, abubuwan da aka samo a hannun wadda ake zargin sun haɗa da kayan abinci guda huɗu da aka riga aka shirya su don amfani, hijabi guda biyu, da kuma agogon hannu guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun sace mataimakiyar shugabar karamar hukuma

Hukumar sojoji ta ce a halin yanzu wadda ake zargin tana tsare a hannun Bataliya ta 196 domin gudanar da bincike na tsanaki da kuma ɗaukar matakin da ya dace.

Sojoji sun cafke mata mai taimakon Boko Haram
Matar da sojoji suka cafke a jihar Borno Hoto: @ZagazolaMakama
Source: Twitter

Majiyoyin sun ƙara da cewa yanayin tsaro a duk faɗin yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali amma ba a san abin da zai iya faruwa ba, yayin da dakarun sojojin suke ci gaba da kasancewa cikin karsashi da ingantaccen shirin yaƙi.

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa sun kai hari wanda ya yi sanadiyyar hallaka sojoji da farar hula a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.

Akalla sojoji bakwai da wani farar hula sun rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kai harin kwanton bauna.

Dakarun sojojin na Operation Fasan Yamma na dawowa ne daga wani samame da suka kai sansanin Lakurawa da ke kusa da iyakar Najeriya lokacin da aka kai musu harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng