NDC: An Gano Wanda Kwankwaso zai Tsayar Ya Fafata da Abba a Kano
- Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso na shirin bayyana sunan wanda zai yi takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Kano
- Da farko an yi tsammanin tsohon 'dan takarar gwamna, Nasiru Gawuna ne zai samu kujerar, sai dai an yi masa tayin mataimakin gwamna
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Gawuna ya ƙi tayin kujerar mataimakin gwamna da ta Sanatan Kano ta Tsakiya kuma ya fadi matsayarsa a NDC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rahotanni sun nuna cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, na dab da bayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdusSalam Gwarzo, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano.
Kwamred Aminu Abdussalam ya sauka daga mukaminsa na mataimakin gwamna a watan Maris, 2026 makonni bayan majalisar dokokin Kano ta aika masa da takardar tsige shi.

Source: Facebook
Jaridar Daily Nigerian ta samu labari daga majiyoyi masu kusanci da lamarin, sun shaida mata cewa an cimma matsayar ne bayan tattaunawa ta sirri da aka yi tsakanin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da abokan siyasa.
Kano: Kwankwaso zai tsayar da dan takara
Tsohon ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, na daga cikin waɗanda ake ganin suna da ƙarfi wajen samun tikitin takarar. Sai dai daga bisani, Kwankwaso ya zaɓi Abdussalam a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026.
Rahotanni sun ce Kwankwaso ya ba wa Gawuna zaɓin karɓar kujerar mataimakin gwamna ko kuma tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya. Amma ana zargin Gawuna ya ƙi tayin biyu tare da alƙawarin yin aiki domin nasarar jam’iyyar.

Source: Twitter
Majiyoyi sun bayyana cewa Gawuna ya shaida wa Kwankwaso cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya ba tare da wani sharadi ba, saboda haka ba zai fice ba saboda rashin samun tikitin gwamna.
Kwankwaso ya yi jinkirin fadin dan takara
Jaridar ta kara da cewa ƙin amincewar Gawuna da tayin da aka yi masa ne ya haddasa jinkirin sanar da Kwamred Aminu Abdussalam a hukumance ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026. Haka kuma, wasu manyan mutane masu tasiri a siyasar Kano na ci gaba da matsa wa Kwankwaso lamba domin ya sake duba matsayarsa, tare da la’akari da irin farin jinin Gawuna a siyasa. Wasu daga cikin masu goyon bayan Gawuna sun ce mafi dacewa shi ne a fito da ɗan takara daga Kano ta Tsakiya domin kalubalantar gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
“Da farko, Gawuna yana da farin jini sosai a Kano ta Tsakiya, inda mafi yawan ƙuri’u suke fitowa. Na biyu kuma, tun da Abba daga Kano ta Tsakiya yake kuma yana wa’adinsa na farko, mafita mafi kyau ita ce a fito da ɗan takara daga yankin domin kada yankin ya ji an tauye shi.”
Majiyar ta ƙara da cewa:
“Wannan shi ne tsarin da NDC ta yi amfani da shi a matakin ƙasa wajen mayar da tikitin shugaban ƙasa zuwa Kudu, tunda shugaban ƙasa daga Kudu ne kuma yana wa’adinsa na farko.”
Sai dai masu goyon bayan Aminu Abdussalam sun ce tsohon mataimakin gwamnan ya nuna jajircewa, biyayya da sadaukarwa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya.
Gwarzo ya magantu kan takara a Kano
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi magana kan sabanin da ya shiga tsakaninsa da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya soki manufar “Kano First” tare da cewa tsaro ya kara tabarbarewa a jihar Kano, inda ya bayyana cewa an dauko tsarin 'yan mulkin mallaka ne inda aka hada wasu yan siyasa a jam'iyyar APC.
Aminu Abdulsalam ya bayyana matsayarsa game da neman kujerar tsohon mai gidansa a jam'iyyar NDC yayin da ke fitar da 'yan takara, inda ya ce zai yi tsarin Kwankwasiyya biyayya.
Asali: Legit.ng


