Kaduna: Bayan Ƙalubalantar EFCC, Kotu Ta Tasa Ƙeyar Ɗan TikTok zuwa Gidan Yari
- Wata kotun tarayya da ke Kaduna ta yanke wa Muhammad Kabir hukuncin dauri saboda cin zarafin Naira a wani bidiyo da ya wallafa
- EFCC mai yaki da masu yi wa tattali zagon kasa ta cafke Kabir bisa zargin take Naira, bayan ya kalubalanci hukumar da ta zo ta kama shi
- Kotu ta yanke masa hukuncin daurin wata shida ko zabin biyan tarar ₦300,000 ga gwamnatin tarayya bisa laifin takekudin Najeriyan a bidiyo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - A ƙarshe, matashin dan TikTok a Kaduna ya san makomarsa bayan hukuncin kotu kan laifin wulakanta Naira a bidiyo.
Wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Kaduna ta yanke wa Muhammad Kabir, hukunci saboda cin zarafin Naira.

Asali: Facebook
Musabbabin cafke matashi ɗan TikTok a Kaduna
Hukumar EFCC ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar da ke yaki da cin hanci ta ce an kama Kabir ne a Tudun Wada da ke jihar Kaduna.
Hukumar ta ce Kabir wanda aka fi sani da @youngcee0066 a manhajar TikTok da Instagram, ya bayyana a bidiyo yana watsar da Naira.

Asali: Twitter
Yadda matashin ya ci zarafin Naira a bidiyo
A cikin bidiyon, an gano shi yana taka Naira a kasa tare da furta kalmomin batanci cikin Hausa, yana kalubalantar EFCC da ta kama shi.
Bayan kama shi, an gurfanar da Kabir a gaban mai shari’a R.M. Aikawa a babbar kotun tarayya da ke Kaduna kan tuhuma daya da aka yiwa gyaran fuska.
Hukumar EFCC ta sha yin gargadi kan cin mutuncin Naira ga ƴan Najeriya inda ta ce babban laifi ne da ya saba dokokin babban bankin Najeriya (CBN)
An karanta masa laifin cewa:
"Kai Muhammad Kabir Sa’ad (wato youngcee0066)(M) wani lokaci a 2025 a Kaduna.
"Cikin ikon wannan kotu mai daraja, ka take Naira ta hanyar taka takardun kudin yayin yin bidiyo sannan ka wallafa a yanar gizo.
"Hakan ya zama laifi karkashin Sashe na 21(3) na Dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wanda hukuncinsa ke karkashin Sashe na 21(1)."
Wane martani wanda ake zargin ya yi?
Kabir ya amsa laifin da aka tuhume shi da shi, sai lauyan gwamnati M.U. Gadaka ya roki kotu ta yanke masa hukunci nan take.
Mai shari’a, Aikawa ya yanke masa hukuncin daurin wata shida a gidan yari ko zabin biyan tarar ₦300,000 ga gwamnatin tarayya bayan wanda ake zargin ya amince da laifinsa.
Kotu ta ɗaure ƴan TikTok a gidan yari
A baya, mun ba ku labarin cewa kotu ta yanke wa wasu fitattun 'yan TikTok biyu, TobiNation da TDollar, hukuncin ɗaurin watanni shida saboda wulakanta Naira a Lagos.
Hukuncin ya biyo bayan kama su tare da gurfanar da su da hukumar EFCC ta yi bisa zargin keta dokar Babban Bankin Najeriya (CBN).
Kotun ta amince da bidiyo da bayanan da EFCC ta gabatar da su a matsayin shaida, kuma ta yanke musu hukuncin ɗauri ko kuma biyan tara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng