Zargin Fyade: ADC Ta Fara Bore bayan Kotu Ta Tasa 'Keyar Dan Takararta zuwa Kurkuku
- Kotu a jihar Ekiti ta tsare ɗan takarar majalisar dokoki na ADC bisa zargin fyade yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da binciken kwakwaf kan zargin
- Rundunar ‘yan sanda ta ce binciken likita ya tabbatar da cewa an yi lalata da wata mata da ta yi zargin ya yi mata dole a wani otal a cikin watan Mayu, 2026
- Matar mai suna Bukola Oluwaseun ta shaida wa 'yan sanda cewa ya jikkata ta a lokacin, kuma binciken farko ya tabbatar da cewa an samu raunuka a jikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ekiti - Wata kotun majistare da ke Ado Ekiti a jihar Ekiti ta bayar da umarnin tsare Ayodele Babatola, ɗan takarar kujerar mazabar Ado 1 a jam’iyyar ADC a majalisar dokokin jihar, bisa zargin fyade.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri
Rahotanni sun ce jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti sun kama Babatola tare da tsare shi kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Abutu Sunday, ya bayyana a wata sanarwa cewa wata mata mai suna Bukola Oluwaseun mai shekaru 30 ta kai ƙarar 'dan takarar.
An shigar da karar dan takarar ADC
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Oluwaseun na zargin Babatola ya yi lalata da ita da ƙarfi a wani otal mai suna Kiibat da ke yankin Adebayo a Ado Ekiti a daren ranar 24 ga watan Mayun 2026.
Mai magana da yawun yan sandan Abutu Sunday ya ce matar ta shaida wa jami’an tsaro cewa an ci zarafinta tare da jikkata ta yayin lamarin, kuma jami’an da suka karɓi ƙorafin sun ga alamun raunuka a jikinta.
A cewar kakakin ‘yan sandan, bayan karɓar ƙorafin ne aka gayyaci wanda ake zargin domin ɗaukar bayaninsa, sannan aka miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar domin zurfafa bincike.

Source: Twitter
Ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa ya fusata ne bayan matar ta buƙaci a biya ta kuɗi kafin ya mu'amalance ta.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Kotu ta kawo karshen shari'ar Jonathan kan takarar shugaban kasa a 2027
Sai dai Sunday ya ce Babatola ya musanta cewa ya yi gama lalata da matar, duk da cewa ya amince ya bar ta a ɗakin otal tare da katse hanyoyin da za ta iya tuntubarsa.
Ana binciken dan takarar ADC a Ekiti
Sunday ya ƙara da cewa an kai matar asibiti domin a yi mata gwajin likita, inda sakamakon binciken ya tabbatar da cewa an abu ya shiga tsakaninsu.
Ya ce:
“Bayan kammala bincike ne aka gurfanar da wanda ake zargin a kotu, kuma yanzu haka yana tsare a cibiyar gyaran hali ta Ado-Ekiti."
A ranar Laraba, 27 ga watan Mayu na shekarar 2026 wasu magoya baya da jiga-jigan jam’iyyar ADC sun gudanar da zanga-zanga a jihar Ekiti domin nuna adawa da tsare Babatola.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai, wani jigo a jam’iyyar ADC mai suna Gboyega Aribisogan ya yi zargin cewa kama da tsare ɗan takarar siyasa ne kawai saboda yana yawan sukar gwamnatin jihar Ekiti.
ADC ta sanar da sakamakon zabe
A baya, kun samu labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na ci gaba da samun nasara a zaben fitar da gwanin jam'iyyar adawa ta ADC da ya kammala.

Kara karanta wannan
Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki
Shugaban kwamitin zaɓen, John Ayuba, ya ce Atiku ya samu nasara a Kano da ƙuri’u 155,595 yayin da Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’u 9,994 gabanin babban zabe da ke tafe a 2027.
Wannan na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya samu nasara a jihohi biyar, lamarin da ya sa ya shiga gaban sauran masu neman takarar shugaban kasa a inuwar hadakar 'yan adawa ta ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng