"A Tattara a Koma Jihar Legas:" Atiku Ya Fara Aika Zafafan Sakonni ga Tinubu

"A Tattara a Koma Jihar Legas:" Atiku Ya Fara Aika Zafafan Sakonni ga Tinubu

  • 'Dan takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa, Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Bola Ahme Tinubu gabanin zaɓen 2027
  • Wanda ya samu tikitin ADC ya ce ya kamata shugaban kasa, Bola Tinubu ya tattara kayansa ya koma Legas domin za a kawo karshen wa'adinsa
  • Atiku ya lashe zaɓen fitar da gwani na ADC da ƙuri’u sama da miliyan 1.8 a shirin da 'yan adawa ke yi na tunkarar babban zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya na ADC, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Atiku ya bayyana cewa lokaci ya yi da Tinubu zai tattara kayansa ya fice daga fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ya koma cibiyarsa ta siyasa a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Zaben fitar da gwani: Yawan kuri'un da Atiku Abubakar ya samu a jihohin Arewa

Atiku ya fara magana game da zaben 2027
'Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Bayo Onanuga
Source: Twitter

The Sun Nigeria tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a Abuja.

Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu

Daily Post ta wallafa cewa 'dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya kamata shugaban kasa Bola Tinubu ya san cewa wa'adinsa na dab da kare wa a shekara mai kama wa.

A cewar Atiku:

“Shugaba Tinubu ya kamata ya tattara kayansa ya koma Legas.”

Ya kuma yaba wa sauran waɗanda suka fafata da shi wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC.

Kalaman Atiku na zuwa ne a lokacin da siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen shekarar 2027, inda manyan jam’iyyu ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen.

Atiku ya doke Amaechi da Hayatu-Deen

Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC bayan ya kayar da sauran masu neman takarar, ciki har da Rotimi Amaechi da Hayatu-Deen.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana tsare tsarensa game da Najeriya bayan lashe tikitin ADC

Atiku ya zama dan takarar ADC a zaben 2027
'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

An bayyana cewa Atiku ya samu ƙuri’a 1,846,370 a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar kwanan nan domin wakilci ADC a zaben 2027.

Sai dai duk da iƙirarin Atiku cewa an gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci, abokan takararsa biyu sun yi watsi da sakamakon zaɓen.

Amaechi da Hayatu-Deen sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaɓen, lamarin da ka iya haifar da sabon rikici a cikin jam’iyyar ADC kafin babban zaɓe na ƙasa.

Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa kalaman Atiku ga Tinubu da kuma yadda aka kammala zaɓen fitar da gwani na ADC za su ƙara ɗaga zafin siyasar Najeriya a watanni masu zuwa.

Atiku ya yi maganar shirinsa ga Najeriya

A baya, mun wallafa cewa 'dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana manyan tsare-tsarensa kan tsaro, ilimi, tattalin arziki da lafiya bayan lashe tikitin shugaban ƙasa na ADC.

Kara karanta wannan

Atiku vs Amaechi: ADC ta sanar da sakamakon zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa a Kano

'Dan takarar ya zargi gwamnatin APC da tauye dimokuraɗiyya da muzgunawa ‘yan adawa a yayin da ya ke furucin godiya bayan 'yan ADC sun zabe shi a matsayin dan takarar da zai wakilce ta.

Atiku ya yi alƙawarin samar da ilimin firamare da sakandare kyauta tare da ɗaukar matakai kan matsalar tsaro da wutar lantarki da a yanzu suke a cikin halin ni 'ya su a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng