EFCC Za Ta Gurfanar da Shahararren Dan Kasuwa Cubana Bisa Zargin Cin Zarafin Naira

EFCC Za Ta Gurfanar da Shahararren Dan Kasuwa Cubana Bisa Zargin Cin Zarafin Naira

  • Hukumar EFCC za ta gurfanar da shahararren dan kasuwa Cubana Chief Priest a gaban kotu ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu
  • Hukumar na zargin shi ne bisa laifin tozarta takardun Naira ta hanyar yin manni da su a wurin taro da aka yi a jihar Legas
  • Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan yanke hukuncin wata 6 wa fitaccen dan daudun nan da aka fi sani da Bobrisky wanda aka kama da laifin tozarta Naira

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Hukumar Yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) za ta gurfanar da wani shahararren dan kasuwa, Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Tuhumar rashawa: Shari'ar gwamnatin Kano da Abdullahi Ganduje ta gamu da cikas

Hukumar za ta gurfanar da shi ne ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024, a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas, bisa zarginsa da wulakanta takardun Naira.

CUbana
EFCC za ta gurfanar da Cubana ne a jihar Legas ranar Laraba. Hoto: Chiefpriiest
Asali: Twitter

A ina za a gurfanar da Cubana?

Za a gurfanar da shi ne a jihar Legas a gaban mai shari’a Kehinde Ogundare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan kasuwan zai yi shari'a da hukumar a kan zarge-zargen aikata laifuka uku da suka sabawa dokar kasa a cewar jaridar Leadership

Laifin da ake zargin Cubana da shi

Laifukan da ake zarginsa da su sun hada yin manni da wulakanta takardun Naira a wani taro, wanda hakan ya saba wa dokar babban bankin kasar na shekarar 2007.

Hukumar ta EFCC ta tabbatar da cewa ana zargin Okechukwu Pascal da cewa a ranar 13 ga Fabrairu, 2024, a Otal din Eko, a lokacin da yake rawa a wani taro ya yi manni da kudade 'yan dari biyar-biyar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Gombe ta dawo da dokar sharar wata-wata

Jaridar Premium Times ta ruwaito EFCC na cewa aikata hakan ya sabawa sashe na 21 (1) na dokar babban bankin kasar ta 2007.

EFCC za ta gurfanar da fitattun mutane

Hakazalika kun ji cewa Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce yanzu haka tana binciken wasu jarumai bisa laifin cin zarafin naira.

EFCC ta sha alwashin gurfanar da wadanda ta kama dumu-dumu da laifin wulakantar da takardun kudin kasar nan gaban kotu domin a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel