An Gurfanar da Sarkin da Ya Bulale Mutanesa kan Gaza Biyan Harajin da Ya Lafta Musu
- Wata kotu a Akure ta gurfanar da basarake a jihar Ondo bisa zargin dukan mutanen da suka ƙi biyan kuɗin haraji da ya lafta musu
- An ce sarkin ya hada kai da wasu mutane biyu inda suka lakadawa mazauna gari duka saboda sun ƙi biyan harajin da suka ce na dole ne
- Har ila yau, an zargi Ojo Olomolekulo da sayar da wani yanki na dajin gwamnati ga wasu mutane biyu daban-daban ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - An gurfanar da wani basarake a jihar Ondo mai suna Ojo Olomolekulo gaban wata kotun majistare a Akure bisa zargin cin zarafin wasu mazauna garin da suka ƙi biyan haraji.
An zargi sarkin da haɗa kai da wasu mutum biyu, Isaac Oloyede da Kehinde Tope, suka lakada wa wasu mutum biyu duka – Iyabo Ajibade da Thompson Owoyemi.

Asali: Original
Rahoto da jaridar the Nation ta wallafa ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne bayan mutanen biyu sun ƙi biyan abin da suka bayyana a matsayin harajin da ba bisa ka’ida ba a yankin.
An gurfanar da sarki a kotun Ondo
Bayan gurfanar da su, lauyan gwamnati, O.A. Iroaye, ya shaida wa kotu cewa ba abin alfahari ba ne a ga wani shugaba na gargajiya ya aikata abin da ake zargin sarkin da shi.
Lauyan ya ce abin takaici ne matuka sarkin ya tilastawa jama’a biyan kudin haraji da kuma cin zarafinsu.
Legit ta rahoto O.A. Iroaye yana cewa:
“Wannan sarkin ya kasance barazana ga zaman lafiyar yankin. Hakan ya nuna gazawar da ba za a iya amincewa da ita ba a matsayin shugaba,”
Sai dai lauyan wadanda ake tuhuma, O.A. Oladunjoye, ya roki kotu da ta ba su beli, inda ya nemi warware rikicin cikin lumana, amma Iroaye ya soki wannan bukata.

Asali: Getty Images
An dage sauraron shari’a zuwa watan Yuni
Alkalin da ke shari’ar, Mai shari’a Taiwo Lebi, ya ba da umarnin cewa sarkin da abokan aikinsa su daina duk wani aiki na karbar haraji daga hannun mazauna yankin.
Ya kuma gargaɗe su da su guji duk wani abu da zai iya haddasa tashin hankali a cikin al’umma, yana mai cewa za a ci gaba da sauraron karar a ranar 20 ga Yuni, 2025.
Hakan ya kara tayar da hankali a yankin Bolorunduro, inda mazauna ke kallon shari’ar a matsayin mataki na dawo da doka da oda a cikin yankin.
'Yan bindiga sun sace sarki a jihar Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun shiga gidan wani sarki a jihar Kaduna.
An ruwaito cewa 'yan bindigar sun sace matar sarkin da 'yarsa sun shiga daji da su ba tare tangarda ba.
Biyo bayan faruwar lamarin, mazauna garin sun roki gwamnati da jami'an tsaro da su taimaka wajen ceto matan da aka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng