Magana Ta Kare, ADC Ta Mika wa Atiku Shaidar Zama 'Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya karbi tutar ADC bayan lashe zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a 2027
- Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya mika wa Atiku tutar a wani taro da aka shirya da yammacin jiya Laraba a Abuja
- A jawabinsa, Atiku ya bukaci sauran wadanda suka nemi tikitin takara da su zo a hada kai domin tabbatar da nasarar ADC a zabe na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam'iyyar adawa ta ADC ta tabbatar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2027.
ADC ta tabbatar da nasarar Atiku a zaben fitar da gwanin da aka gudanar ta hanyar mika masa tutar jam'iyya a matsayin shaidar zama dan takararta a zabe na gaba.

Source: Facebook
Atiku ya karbi tutar jam'iyyar ADC
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya karɓi tutar jam’iyyar a hukumance a wani taro da aka shirya a Abuja, kamar yadda The Nation ta rahoro.
An gabatar masa da tutar ne a Abuja a yammacin ranar Laraba bayan kammala tattara sakamakon zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da aka gudanar a faɗin ƙasar nan ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026.
Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ne ya miƙa wa Atiku tutar a gaban shugabannin jam’iyya da dandazon magoya baya.
David Mark ya buƙaci haɗin kai
Da yake jawabi yayin taron, David Mark ya ce:
“Zan miƙa tutarmu ga wanda zai jagorance mu zuwa Aso Rock. Abin da ke gaba ba zai kasance mai sauƙi ba, amma tare da goyon bayan ‘yan Najeriya za mu yi nasara.
"‘Yan Najeriya na kallonmu domin ganin ko za mu iya yin abin da ya dace da su. Ina fatan wannan ya zama sabon farawa na aminci a siyasa.”
Ya kuma yi kira ga sauran wsdanda suka nemi takara da su haɗa kai, yana mai cewa dukkansu sun cancanci jagorantar ƙasar nan, cewar rahoton Vanguard.

Source: Facebook
Atiku ya yi jawabin karbar takara
Da yake jawabin karbar takara, Atiku ya bayyana cewa ya amince zai yi wa ADC takarar shugaban kasa a zaben 2026, inbda ya ce, "na amince da wannan takara."
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya buƙaci sauran masu neman tikitin jam’iyya, Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen, da su haɗa kai domin ci gaban jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya samu ƙuri’u 1,846,370 a zaɓen fitar da gwanin yayin da Amaechi ya samu ƙuri’u 504,117, Mohammed Hayatu-Deen ya samu ƙuri’u 177,120.
Atiku ya dura kan Shugaba Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya dura kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana cewa lokaci ya yi da Tinubu zai tattara kayansa ya fice daga fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ya koma cibiyarsa ta siyasa a jihar Legas.
Kalaman Atiku na zuwa ne a lokacin da siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen shekarar 2027, inda manyan jam’iyyu ke ƙara shiri domin tunkarar zaben.
Asali: Legit.ng

