Ta'addanci: Matasa Sun Yi Bore a Kano, Sun Kona Wani Ginin Gwamnati

Ta'addanci: Matasa Sun Yi Bore a Kano, Sun Kona Wani Ginin Gwamnati

  • Wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kano domin jawo hankalin gwamnatin Abba Kabir Yusuf game da rashin tsaro
  • Matasan sun fara zanga-zangar a matsayin ta lumana, amma daga baya lamarin ya rikide zuwa tashin hankali a karamar hukumar Gwarzo
  • Zanga-zangar da suka yi ta biyo bayan karuwar ayyukan 'yan ta'adda da ake samu a Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo inda aka kashe mutum 2

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wasu fusatattun matasa a Karamar hukumar Gwarzo da ke jihar Kano sun banka wa ofishin shugaban karamar hukumar wuta, yayin da suke zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar yankin.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan da matasan suka fito kan tituna suna nuna bacin rai kan hare-haren ‘yan bindiga da ke yawaita a kauyukan yankin.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Malamin addini da matarsa sun mutu a hatsarin jirgin ruwa

Matasa sun yi zanga-zanga a Kano
Taswirar jihar Kano inda aka yi zanga-zangar adawa da ta'addanci Hoto: Legit.ng
Source: Original

A ruwayar jaridar Daily Trust, matasan sun nufi sakatariyar karamar hukumar ne daga kauyukansu da kafa, domin isar da koke kan halin da suke ciki.

An yi zanga-zanga a Kano

A labarin da Trust Radio ta wallafa, ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Lakwaya da ke cikin Gwarzo a ranar Juma’a, 15 ga Mayu, 2026, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga kauyen ne a kan babura sama da 30, suna harbi ba kakkautawa, lamarin da ya tayar da hankali a tsakanin mazauna.

Wani mazaunin yankin, Ismail Aliyu Gwarzo, ya shaida wa jaridar cewa matasan sun yi tattaki mai nisan kusan kilomita 20 zuwa sakatariyar karamar hukumar domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara.

Matasan sun yi kone-kone a yayin zanga-zanga
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a lokacin da ya ke jawabi a wani taro Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cewarsa:

“Mutanen kauyuka sun yi tafiyar kusan kilomita 20 zuwa sakatariya domin yin zanga-zanga kan yawaitar matsalar tsaro a yankunansu. Sun lalata wasu kadarori sannan suka banka wa wani bangare na ofishin wuta. Lamarin ya haifar da fargaba, inda jama’a suka rika guduwa don tsira da rayukansu.”

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun aikata ta'asa, sun sace shugaban makaranta da dalibai masu yawa a Oyo

Kano: Zanga-zangar lumana ta koma tashin hankali

Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka lalata kayayyaki tare da kona ofishin shugaban karamar hukumar.

Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko jami’an tsaro dangane da lamarin da ya tayar da hankulan mazauna yankin.

Sai dai wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an aika jami'an tsaron kwantar da tarzoma domin a shawo kan matsalar kafin ta gagari kundila.

Lamarin ya kara nuna irin damuwar da ke karuwa a tsakanin al’umma kan matsalar tsaro a yankunan karkara, musamman a Arewacin Najeriya.

Wani hari a Kano ya jikkata bayin Allah

A baya, mun kawo labarin cewa 'yan bindiga sun kai hari ƙauyen Yankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano, inda suka kashe mutum biyar bayan sun tayar da hankula da harbe-harbe.

Harin ya auku ne da kusan 5.30 na yamma, inda maharan suka fito daga maƙwabciyar jihar Katsina suka buɗe wuta ba kaukautawa tare da jikkata mutanen da ke harkokinsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27

Shugaban ƙauyen Yankamaye, Sunusi Abubakar, ya tabbatar da cewa maharan sun sace adadi mai yawa na dabbobi kafin su tsere daji yayin da aka kaw wadanda suka jikkata zuwa Kano don karban magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng