Yadda Umarnin Trump na Kare Kiristocin Najeriya Ya Yi Nasarar Kisan Yan Bindiga

Yadda Umarnin Trump na Kare Kiristocin Najeriya Ya Yi Nasarar Kisan Yan Bindiga

  • Ma'akatar tsaron Amurka ta yi magana kan umarnin da shugaban kasar, Donald Trump ya ba ta game da kare Kiristoci a Najeriya
  • Sakataren yaƙin Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa haɗin guiwar sojojin Najeriya da Amurka ya kashe Abu-Bilal al-Minuki a yankin Tafkin Chadi
  • Hegseth ya ce bayanan sirri da aka tattara yayin farmakin sun taimaka wajen kashe daruruwan mayaƙan ISIS da ke kai hare-hare kan Kiristoci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ministan tsaro a Amurka, Pete Hegseth ya bayyana damuwa game da ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a Najeriya.

Hegseth ya ce shugaba Donald Trump ya umurce su da su taimaka wajen kare Kiristocin Najeriya daga hare-haren mayakan ta’addanci masu alaƙa da ISIS.

An gano musabbabin hallaka manyan yan ta'adda da Amurka ta yi a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga, Maxine Wallace/The Washington.
Source: Getty Images

Ya ce haɗin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka ya kai ga kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban ISIS na biyu, cewar Fox News.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Umarnin Trump na kare Kiristoci a Najeriya

Hegseth ya bayyana cewa bayanan sirri da aka samu daga aikin sun taimaka wajen kashe daruruwan mayaƙan ISIS masu kai hare-hare kan Kiristoci a Najeriya.

Ya ce:

“Wataƙila kusan shekara guda da ta wuce, an ji kukan Kiristocin Najeriya da ISIS ke kai wa hari tare da kashe su a Najeriya, sai ya ce, ‘Pete, ina son ma’aikatar yaƙi ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa mun yi duk abin da za mu iya domin kare waɗannan Kiristocin.”

Ya ce gwamnatin Trump ta jajirce wajen yaƙi da ta’addanci tare da kare al’umma masu rauni daga hare-haren kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a duniya.

Gwamnatin Amurka ta magantu kan kokarin kare Kiristocin Najeriya
Shugaba Donald Trump na Amurka lokacin kamfe a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Yadda aka yi nasarar kashe Al-Minuki a Najeriya

Rahoton ya ce an kashe Abu-Bilal al-Minuki a wani farmaki na haɗin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka a Arewa maso Gabashin Najeriya cikin watan nan.

Hegseth ya kara da cewa bisa bayanan sirri da suka tattara, sun kashe daruruwan mayakan ISIS da ke kai hare-hare tare da kashe Kiristoci a Najeriya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar sulhu da Iran, ya fadi makomar mashigar Hormuz

Ministan tsaron Amurka ya bayyana aikin a matsayin wani bangare na kudurin gwamnatin Donald Trump na yaki da ta’addanci da kuma kare al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali.

“Saboda haka akwai abubuwa da dama da muke yi da kafafen yada labarai suke mayar da hankali a kansu, sannan akwai wasu abubuwan da shugaban kasa ke bai wa ma’aikatar damar yi a madadin al’ummar Amurka wanda ya cancanci yabo sosai saboda su."

- In ji Hegseth.

Kisan Kiristoci: Trump ya yada bidiyon fasto

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya yada wani faifan bidiyo da fasto a Najeriya ke neman taimakonsa kan zargin kisan Kiristoci.

Fasto Ezekiel Dachomo ya yi kira ga Trump da Majalisar Dinkin Duniya su taimaka wajen dakatar da abin da ya kira kisan kare dangi.

Sake wallafa bidiyon ya zo ne bayan Trump ya sanar da kashe wani babban kwamandan ISIS a hadin gwiwar sojojin Amurka da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.