
Shafukan ra'ayi da sada zumunta







Mutane da dama sun soki Gwamna Uba Sani na Kaduna da ya taya Nasir El-Rufai murnar zagayowar haihuwarsa, yana mai masa fatan alheri da kariya daga Allah.

Kamfanin MTN ya bayyana cewa ya san bai kyauta wa abokan hulɗarsa ba, saboda haka an janye ƙarin farashin data da aka wayi gari da shi a ranar Alhamis.

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta bayyana cewa akwai bukatar a samu karin mutanen da ke dawo da 'yan uwansu hanya idan sun tasamma lalacewa don gyara al'umma.

Wata daliba a Jami’ar UNIZIK ta ciji malami bayan sun samu sabani kan daukar bidiyon TikTok. Jami’an tsaro sun fara bincike kan don gano gaskiyar lamarin.

Kamfanin sadarwa na MTN ya fara aiwatar da karin kaso 50% kan kudin data. Kamfanin na MTN ya kara farashi kan yadda yake siyarwa 'ƴan Najeriya data.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ya tallata Tinubu a 2023 don Allah, ƙasa da jam'iyya, ba don wata riba ba, yana mai cewa komai ya wuce a yanzu.

Yayin da wasu fusatattun 'ya'yan jam'iyyar APC ke sukarta, shugabanninta a Arewa ta Tsakiya sun gargade su kan cin mutuncin Bola Tinubu da sauran jiga-jiganta.

Bayan yan uwan dan TikTok mai yada badala sun hukunta shi, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jinjina musu inda ya bukaci a yi koyi da su cikin al'umma.

Wani dan Arewa a shafin sada zumunta ya nuna goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hakan ya sanya mutane da dama sun yi masa rubdugu.
Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Samu kari