Rai Bakon Duniya: Fitaccen Basarake a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi alhinin rasuwar babban basarake wanda ya ba da gudummawa mai yawa
- Marigayin wanda shi ne Alawe na Ilawe Ekiti, Oba Adebanji Alabi ya yi bankwana da duniya ne bayan fama da rashin lafiya
- Oyebanji ya bayyana marigayin a matsayin ma’ajiyar tarihi, ilimi da al’adu, wanda mulkinsa ya kawo zaman lafiya da ci gaba a Ilawe Ekiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ado-Ekiti, Ekiti - Al'ummar jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya sun shiga alhini bayan rasuwar wani fitaccen basarake a jihar.
Gwamna, Biodun Oyebanji, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Alawe na Ilawe Ekiti, Oba Adebanji Alabi.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Yinka Oyebode, ya fitar a shafin Facebook a ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2026 da muke ciki.
Gwamna ya jajanta kan rasuwar babban basarake
Sanarwar ta ce gwamnan ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da mutanen Ilawe Ekiti wanda ya daga hankalin mutanen yankinsa saboda gudummawar da ya ke bayarwa.
Oyebanji ya bayyana marigayin a matsayin ma’ajiyar ilimi, tarihi da al’adu, yana cewa ya kasance shugaba mai kishin jama’arsa da ci gaban al’ummarsa baki daya.
Ya ce mulkin marigayin ya kasance cikin zaman lafiya da ci gaba, wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa Ilawe Ekiti da sauran yankunan jihar Ekiti.
Gwamna ya tuna alherin da marigayin ya shuka
Gwamnan ya ce jihar ta yi babban rashi saboda mutuwar sarkin, yana mai cewa ya bar gibin da zai yi wahalar cikewa nan gaba.
Oyebanji ya tuna cewa Oba Alabi ya taba zama shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar Ekiti tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021 cikin kwarewa da mutunci.
A cewarsa, marigayin ya bayar da gudunmawa sosai wajen tafiyar da harkokin gwamnati ta hanyar shawarwari masu amfani da kuma gogewarsa wajen warware rikice-rikice.

Source: Original
Gudunmawar da marigayin ta ba al'ummar Ekiti
Gwamnan ya kara da cewa marigayin ya kasance mai fitacciyar murya a matakin kasa kan batutuwan da suka shafi Najeriya da ci gaban al’umma baki daya.
Ya ce marigayin yana da salo na musamman wajen bayyana ra’ayoyinsa a tarurruka da daban-daban, lamarin da ya sa mutane da dama suke girmama shi.
Oyebanji ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalan marigayin, sarakunan gargajiya, abokansa da daukacin mutanen Ekiti hakurin jure wannan babban rashi mai raɗaɗi.
Alkalin babbar kotun tarayya ya rasu a Kano
A wani labarin mai kama da wannan, an ji cewa alƙalin babbar kotun tarayya reshen Jihar Kano, Mai Shari'a Mohammed Nasir Yunusa ya rasu bayan ya fadi a falon gidansa.
Daraktar yaɗa labarai ta Kotun Tarayya ta Najeriya, Catherine Oby Christopher, ta ce Mai Shari'a Yunusa ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano.
Marigayi alkalin ya jagoranci manyan shari'o'i a rayuwarsa ciki har da batun halascin shiga zaben 'yan takarar jam'iyyar LP a 2023.
Asali: Legit.ng

