'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Garuruwan Benue, An Bi Mutane har Gida An Kashe Su

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Garuruwan Benue, An Bi Mutane har Gida An Kashe Su

  • 'Yan bindiga sun kai hari kan kananan hukumomin Gwer ta Yamma da Buruku a jihar Benue, inda suka kashe mutane bakwai
  • An kashe mutane biyu a Gwer ta Yamma a kan hanyar Adoka-Makurdi, yayin da aka bi wasu biyar har gidajensu aka kashe su a Buruku
  • Shugabannin kananan hukumomin sun tabbatar da faruwar lamarin, har ma an bada umarnin takaita zirga-zirga a Gwer ta Yamma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - An ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe mutane bakwai a safiyar ranar Litinin a yankuna daban-daban cikin kananan hukumomi biyu na jihar Benue.

Rahoto ya nuna cewa an kashe biyu daga cikin wadanda abin ya shafa wajejen karfe 7:00 na safiya a kan hanyar Adoka-Naka-Makurdi a karamar hukumar Gwer ya Yamma.

'Yan bindiga sun kashe mutane 7 a sabon harin da suka kai garuruwan jihar Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Iormem Alia. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

An ce 'yan ta'addar sun bi wasu mutum biyar har gida sun kashe su wajen karfe 1:00 na dare a karamar hukumar Buruku, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe mutane 7 a hare-haren Benue

Mazauna yankin sun ce maharan sun afka wa al'ummar Mbakundu a cikin gundumar Mbaya ta karamar hukumar Buruku a tsakiyar dare, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

Wani ganau, mai suna Kaase, ya ce an gano gawawwaki biyar, ciki har da ta karamin yaro, da Asubahi, yayin da ake ci gaba da neman wasu da har yanzu ba a gansu ba.

“Yanzu haka da muke magana, an samu gawarwaki biyar, ciki har da karamin yaro. Har yanzu muna neman wasu da suka bata a lokacin harin,” inji Kaase.

Shugaban karamar hukumar Buruku, Raymond Aondoakura, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin ta hanyar sakon tes.

Jaridar Tribune ta rahoto Aondoakura yana cewa:

“Eh, sun kashe samari hudu da karamar yarinya daya. Ya zuwa yanzu, an gano gawawwaki biyar kuma an kai su dakin ajiye gawa.”

An sanya dokar takaita zirga zirga a Gwer

Hakazalika, shugaban karamar hukumar Gwer ta Yamma, Victor Ormin, ya shaida wa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an kashe mutane biyu a yankinsa a safiyar Litinin.

Ormin ya kara da cewa saboda rashin tsaro, ya bada umarnin takaita zirga-zirga, musamman ta shige da fice a karamar hukumar daga karfe 6:30 na yamma.

“Wannan umarnin ya fara aiki nan take. Ya zama dole mutanen da ke shigowa karamar hukumar Gwer ta Yamma da wadanda ke fita su yi hakan kafin karfe 6:30 na yamma.
"Za a sake duba wannan doka ta takaita zirga-zirga yayin da yanayin tsaro ya inganta a karamar hukumar."

- Victor Ormin.

'Yan bindiga sun addabi garuruwan Benue da hare-hare
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Benue. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mutane 166 'yan bindiga suka kashe a Benue

Kisan kiyashin na baya-bayan nan ya kawo adadin mutanen da aka kashe a hare-haren 'yan bindiga a jihar Benue tsakanin 1 ga Afrilu zuwa 12 ga Mayu, 2025, zuwa 166 cikin kwanaki 41.

A halin da ake ciki, babban daraktan tsaron cikin gida na jihar, Air Commodore Jacob Gbamwuan (mai ritaya), ya ce ya samu labarin faruwar lamarin ne kawai kuma har yanzu bai samu cikakkun bayanai ba.

Har yanzu kakakin 'yan sandan jihar Benue, CSP Catherine Anene, ba ta amsa kira ko mayar da amsar sakonni ba a lokacin hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun mamaye Benue' - Gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Hyacinth Alia ya nuna matuƙar damuwarsa game da ƙaruwar matsalolin tsaro a Benue, musamman yanzu da damina ke gabatowa.

Ya bayyana cewa akwai wasu miyagu da ke ƙoƙarin fatattakar mutane daga garuruwansu don su mallake su, saboda haka ya roƙi gwamnatin tarayya da ta kawo musu ɗauki.

Gwamnan Benue ya yi kashedi ga 'yan siyasar da ke amfani da wannan rikicin, ya kuma bayyana cewa duk wanda aka samu da laifi ɗan ta'adda ne kuma za a fallasa shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.