'Yan Bindiga Sun Kai Hari Arewa, Sun Kashe Babban Kusa a Jam'iyyar APC da Wasu 3
- 'Yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe jigon APC, Akaabo Johnson da wasu mutum uku a garuruwan jihar Benue
- Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne da misalin 4:35 na yammacin Talata, suka bude wuta kan mai uwa da wani
- Ciyaman din Gwer ta Gabas, Timothy Adi ya yi tir da wannan harin, yana mai cewa wannan karo hari na biyu a cikin makwanni biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC, mai suna Akaabo Johnson da wasu mutane uku.
An ce 'yan bindigar sun kashe jigon APC da mutanen uku ne a harin da suka kai garuruwan Mbalom da Mbasombo a karamar hukumar Gwer ta Gabas, jihar Benue.

Asali: Original
'Yan bindiga sun kai hari a Benue
A cewar mazauna yankin, 'yan bindigar sun farmaki garuruwan biyu ne da misalin karfe 4:35 na yammacin ranar Talata, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shaida cewa 'yan bindigar sun yi jama'ar garuruwan kwanton bauna, kafin daga bisani suka bude wuta kan mai uwa da wani, lamarin da ya zama silar mutuwar mutane huɗu.
Shugaban karamar hukumar Gwer ta Gabas, Timothy Adi, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Laraba.
Timothy Adi ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kai harin ne a lokacin al'umma ba su yi zato ko tsammani ba.
An kashe jigon APC a harin Benue
Shugaban karamar hukumar, wanda ya yi tir da ayyukan 'yan bindigar a yankin, ya ce harin na ranar Talata shi ne na biyu cikin makwanni biyu da suka gabata.
Ya ce an tura jami'an tsaro yankin don tabbatar da tsaron iyakokin karamar hukumar, da nufin hana afkuwar wasu karin hare-haren.
Timothy Adi ya ce:
“An gano gawarwaki huɗu ciki har da ta wani dattijo, wanda babban jigon jam'iyyar APC ne a yankin kuma an kai gawarwakinsu dakin ajiye gawa na asibitin St. Gregory.
“Ina kira ga mazauna yankin, musamman matasa, da su kasance a ankare kuma su kai rahoto ga hukumomin tsaro game da duk wani motsi da ba su yarda da shi ba."

Asali: Twitter
An yabawa Gwamna Hyacinth Alia
Shugaban karamar hukumar ya ce dole ne al'ummomin da abin ya shafa su hada kai, yayin da ya ce Gwamna Hyacinth Alia yana iya kokarinsa na kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.
Timothy Adi ya yabawa Gwamna Alia bisa matakan da ya ke dauka da kuma goyon bayan da ya bayar na tura jami'an tsaro cikin gaggawa don shawo kan lamarin.
Ƙoƙarin da aka yi don samun kakakin rundunar 'yan sandan Benue, Catherine Anene, don tabbatar da wannan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin hada rahoton.
'Yan bindiga sun hallaka mutane a Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari a ƙaramar hukumar Otukpo da ke jihar Benue.
Maharan sun kai wannan hari ne a yammacin ranar Talata, 15 ga Afrilu, 2025, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.
Harin da 'yan bindigan suka kai a ƙauyen Otobi ya jawo wasu mutane da dama sun raunata, yayin da ake kokarin sanin adadin wadanda harin ya shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng